Ga Duk Abinda Ya Kamata Ku Sani Game da Tarihin Aisha soba
Kannypedia tayi nazari sosai wajen kawo muku muhimman Bayanai dangane da Tarihin Aisha Soba, Rayuwarta, Aure, Fina Finai dasauransu.
Takaitaccen Bayani
| SUNA | Aisha Soba |
|---|---|
| INKIYA | Aisha Soba |
| SHEKARU | 28 aprilu 2007 ( shekaru 19years Yanzu 2026) |
| AIKI | Jaruma |
| YARE | Hausa |
| MAZAUNIN | Kaduna, Nigeria |
| AURE | Aisha soba batai Aure Ba ( 2026 ) |
| YARA | Babu |
| Fina finai | Sama da Ashirin (10+) |
| SOCIAL MEDIA | TikTok: Aisha Soba Instagram: Aisha soba YouTube: Aisha Soba Tv |

Wacece Aisha Soba?
Aisha Soba matashiya ce kuma fitacciya a masana’antar Kannywood, wacce ta yi suna musamman a matsayin yar rawa a wakokin Hausa kafin daga bisani ta koma harkar fim.
Kamfanin Arewa Medium ne ya fito da jarumar yakuma gabatar da ita a Matsayin jaruma dakuma daukar nauyin hadata da wasu manyan taurari domin yin Aiki da ita.
Aisha soba Ta shahara sosai saboda kwarewarta wajen rawa, kwalliya da kuma iya bayyana rangwada a tafiyarta da a cikin fina-finai.
Soba tafara ne da hawa kan wakokin hausa inda take nuna fasahar da Allah yayi mata na iya tafiya da take dashi.
Hakan yasa ta jawo hankalin dubun nan daruruwan al’umma suka Fara bibiyar shafin ta.
Daga cikin Fina finain da Aisha soba tafito Akwai shrin har abadan wadda kamfanin Arewa Medium ya shiryawa jarumar, sai fim din shatu dakuma fin din Dammy & Ammy.
Haihuwa Da Farkon Rayuwa
An haifi jaruma Aisha Soba a ranar 28 ga watan Aprilu shekarar 2007 a garin Kaduna dake arewacin kasar Najeriya.
Soba Ta taso a kaduna kuma ta yi karatunta na matakin primari dakuma na sakandari duk a kaduna kamin nan shigowarta masana’antar shirya Fina finan hausa.
Aisha soba na Daga cikin mata wadanda suka shahara saboda kyawunsu da Kuma iya motsa jiki musamman wajen rangwada, sannan tana Daga cikin mata da suka samu Daukaka lokaci daya.
Tana fitowa cikin wakoki wadanda mawaka hausa suke rerawa Kuma su daura a YouTube mawaka kaman
- Umar mb
- auta mg
- ado gwanja dasauransu.
Yadda Ta Aisha Soba Fara Fim A Masana’antar Kannywood
Jarumar ta Fara sha’awar harkar fim tin tana karama Amma Bata samu daman shigowa ba har saida ta kammala karatunta.
Aisha soba ta farane da zama model karkashin kamfanin Arewa Medium a shekarar 2023.
Daga baya Aisha Soba ta fara fitowa a matsayin yar rawa a wakokin Hausa, inda take bayyana a cikin bidiyon wakoki daban-daban na mawakan hausa.
kamar yadda muka ambata a baya Kamfanin shirya fina-finai na Arewa Medium ne ya gano basirarta tare da ba ta dama a wasu shirye-shirye da fina-finai, wanda hakan ya bude mata kofar shiga Kannywood.
Jarumar tashigo da kafar dama domin tasamu karbuwa lokaci Daya, kana iya cewa tana cikin matan da suka Shahara a shekararsu na farko da shigowarsu kafar sada zumunta na tiktok.
Yadda Aisha Soba Ta Yi Fice
Ta fara samun shahara ne bayan fitowarta a wakokin Hausa da suka yi tashe musamman Wanda Mawaki Umar mb yake rerasu kamar su RUHI waka mai dogon zango.
Wadanda aka saki bidiyon a shekarar 2024 tareda soja boy kuma aka daura a manhajar YouTube channel din Umar mb.
Tin bayan fitowarta cikon wakar Ruhi Al’umar hausa suka ga baiwar da Allah yayi mata na Kyau dakuma kwarewar aiki.
Hakan yasa masoya suka fara lura da ita saboda salon rawar da ta taka cikin Shirin bidiyon wakar.
Cikin wakoki dasuka sanya Aisha soba yin fice Akwai wakar Kauna ta Umar mb wadda ya sanya soba cikin bidiyon wakar.
Daga bisani, fitowarta a fim din shatu ya kara daga darajarta, har ta fara zama daya daga cikin matasan jarumai masu tasowa a masana’antar kannywood.
Wakar nan ta auta mg boy mai suna makauniya tasa Aisha soba yin matukar fice fiye da ko wacce wakoki datahau domin wakar tasamu makallata sama da miliyan suka kalla a manhajar YouTube.
Aikace-Aikacenta
Jerin Fina-finain Aisha Soba (Kannywood)
Kasancewar soba sabuwar jaruma a masana’antar kannywood batai Finai dayawaba.
Amma tafito cikin manyan fina finai kamar su: shatu tareda shamsu Dan’iyaz
2025, Tarayya tareda Kamala S Fulani, Abdullahi Abbas 2025, Har abada 2026, Zuciya Da Fata Da sauransu
Jerin Fina Finan Aisha soba da bidiyon wakar Aisha soba
| Jerin fim da wakar Aisha Soba | Nau'in Fim |
|---|---|
| shatu | Shiri mai dogon zango ( series) |
| Tarayya | Shiri mai dogon zango ( series) |
| Aminatu | Shiri mai dogon zango ( series) |
| Zuciya Da Fata | Shiri mai dogon zango ( series) |
| Har abada | Shiri mai dogon zango ( series) |
| Sakacina | Shirin mai dogon zango (series) |
| Soyayya Ta | Bidiyon waka |
| Ruhi tareda Umar mb | Bidiyon waka 2024 |
| Halitta wakar Umar mb | Bidiyon waka 2024 |
| Zuciya wakar habeb taku | Bidiyon waka 2025 |
| Makauniya wakar auta mgboy | Bidiyon waka 2025 |
| Dan asalin ft aura waziri | Bidiyon waka 2025 |
| Mai asali wakar auta mgboy | Bidiyon waka 2026 |
| Taurari tareda aura mg boy, Umar mb, Maryam Hussaini, auta waziri meleri, Amal umar | Bidiyon waka 2015 |
| Mai kyau ft Umar mb | Bidiyon waka 2025 |
Bidiyon Wakokin Aisha Soba
Kamar de yadda muka lissafa Aisha Soba ta fito a wakoki tare da mawaka da dama, musamman a matsayin yar rawa.

Karanta: CIKAKKEN TARIHIN FATIMA HUSSAINI (Maryam Labarin)
Hadaka Da Jarumai Da Mawaka
Ta yi aiki tare da jarumai da mawaka daban-daban a Kannywood, wanda hakan ya taimaka mata wajen kara samun suna da kwarewa a harkarta.
Jerin wadanda tayi Aiki dasu Akwai:
- Umar mb
- Auta mb
- Auta waziri
- Shamsu Dan iya
- Fatima hussaini
- meleri
- habeb taku
- Hauwa ayawa
- Kamal s fulani Dasauransu
Kyaututtuka Da Nasarori
Duk da kasancewarta sabuwa a masana’antar, Aisha Soba ta fara samun yabo daga masoya saboda:
Kwarewa a rawa, Kyakkyawan kwalliya, Hazaka a fim da sauran hanyoyin Jan hankalin al’umma hakan yasa ake sa ran za ta samu manyan kyaututtuka nan gaba.
Rayuwar Soyayya Da Bayani Na Musamman
A halin yanzu ba ta bayyana wani saurayi ko aure ba sannan Babu wani da ya bayayana Yana kasancewa da iya Idan ba abokan aikinta ba.
Wasu Bayanai Game Da Ita:
Tana son kwalliya da daukar hoto sosai hakan yasa tayi fice wajen nuna hakan wa duniya hausawa
SHAWARA GA MASU SHIGOWA KANNYWOOD
Aisha Soba na baiwa masu tasowa shawara da su: su yi hakuri su dage wajen koyon aiki su guji abubuwan da za su bata musu suna
SHAFUKAN SADARWA
Instagram: Aisha soba
TikTok: Aisha soba
Youtube: Arewa medium
Qarin Bayani
Aisha Soba na daga cikin sabbin jarumai masu tasowa a Kannywood, musamman a bangaren rawa da wakoki. Tare da goyon bayan kamfanin Arewa Medium, tana ci gaba da kafa suna a masana’antar nishadi ta Arewa, kuma ana sa ran za ta zama babbar jaruma nan gaba.
Tarihin Aisha Soba
Kannypedia tayi nazari sosai wajen kawo muku muhimman Bayanai dangane da Tarihin Aisha Soba ku cigaba da bibiyarmu domin sabunta Bayani a bayan lokaci.
