‎CIKAKKEN TARIHIN FATIMA HUSSAINI (Maryam Labarin)

Ga Duk Abinda Ya Kamata Ku Sani Game da Tarihin Fatima Hussaini (Maryam labarina).

Kannypedia tayi cikakken nazari Dan kawo muku muhimman Bayanai dangane da Tarihin Fatima Hussaini , Saurayi, Gari, Fina finai da sauransu.

Takaitaccen Bayani

SUNAFatima Hussaini Abbas
INKIYAMaryam Labarina
SHEKARU3 January 1998 ( shekaru 28 Yanxu 2026)
AIKIJaruma, Marubuciya, mai shirya fim
YAREBabur, Hausa
MAZAUNINKaduna, Nigeria
AUREMaryam labarina batai Aure Ba ( 2026 )
YARA Babu
Fina finaiSama da Ashirin
(10+)
SOCIAL MEDIATikTok: fateeema hussaini
‎Instagram: fateeema_hussain
YouTube: fateeema hussaini Tv
Fatima Hussaini
Fatima Hussaini tareda Aisha soba

‎Wacece Fatima Hussaini?

‎Fatima Hussaini fitacciyar jaruma ce a masana’antar shirya Fina finain hausa da akekira da Kannywood.

Anfi sanin Jarumar da suna Maryam labarina saboda rawar da ta taka cikin shirin mallam aminu saira mai dogon zango me suna labarina.

Fatima Hussaini ta shahara sosai ta hanyar fitowarta a shahararren shirin nan mai dogon zango mai suna Labarina, hakan yasa ake kirana  da suna Maryam Labarina.

‎Ba kawai jaruma ba ce, har ila yau marubuciya ce kuma mai shirya fina-finai, wacce take amfani da iliminta na boko wajen kawo sabbin tsare-tsare a harkar fim.

Fatima Hussaini (Maryam labarina) ta jagoranci manya manyan fina finai na hausa tin kamin tadau lokaci mai tsawo da shigowarta masana’antar shirya fim na kannywood.

Daga cikin manyan fina finai data jagoranta Akwai:

  • labarina wadda mallam aminu saira ya shirya
  • wata shaida
  • Na ladidi da sauransu.

Jarumar na cikin Jarumai da suka samu Shahara cikin kankanin lokaci saboda kwarewarta dakuma hazakarta hakan yasa take da tarun mabiya a duniyar hausawa.

A shekarar 2026 ne Fatima Hussaini tafara shirya fim (producing) fim nata na kanta a fim din Dammy & Ammy wanda itace ta rubuta Kuma ta shirya shi.

Jarumai da suka fito cikin Shirin sune farida Abdullahi, Fatima Hussaini, Alameen Ay dasauransu, sannan an saki Shirin ne YouTube channel dinta mai suna fateeema hussaini Tv.

‎Haihuwa Da Farkon Rayuwa

Cikakken sunanta Fatima Hussaini Abbas Amma anfi saninta da suna (Maryam labarina) Iyayen Asalin Yan jahar Borno ne dake Gabas maso arewacin Nigeria.

‎An haifi jaruma Fatima Hussaini a garin Jos a ranar 3 ga Januaru shekarar 1998, Daga bisani iyayenta suka kaura Zuwa Abuja.

A can tayi karatu Daga Matakin primary 1 Zuwa primari 2, sai suka dawo kaduna ta kammala karunta a makarantar Betty Queen International school.

‎Daga bisani Maryam labarina Tayi karatun diploma sannan tayi Hnd a fannin Science laboratory technology (SLT) a makarantar politechnic dake garin Zaria a jahar kaduna.

‎An san ta da son karatu sosai, wanda hakan ya taimaka mata wajen fahimtar rubutu da tsara labarai fagen harkar fim.

‎Yadda Maryam Labarina Ta Shiga Masana’antar Kannywood

‎Fatima Hussaini ta fara harkar fim ne ta hanyar rubuce-rubuce (script writing), kafin daga bisani ta fara fitowa a matsayin jaruma Daga cikin labarin Fina finain data rubuta a wancan lokaci Akwai Sirrin kyau, amaryar boye dasauransu.

‎Hazakarta da ilimi suka sa ta samu damar shiga manyan ayyuka cikin sauki, musamman a shirye-shiryen da ke bukatar basira da fahimta.

‎Tashiga masana’antar fim ne ta hanyar me shirya fina finai a manhajar YouTube me suna mazaje ne a fim dinsa mai suna sirrin kyau Wanda shine Shirin ta nafari Kuma itace marubuciyar Shirin.

Ganin gudumawar data bayar a Shirin Sirrin kyau ne hakan Yaja ra’ayin dayawa cikin masu shirya fim din hausa har sukayi sha’awar sata a nasu Shirin.

‎Daga bisani fatima hussaini ta fito a fina finai dadama kamar su fatake, amarya, Na ladidi, makarantar farko, labarina dasauransu.

Fatima Hussaini (Maryam labarina) itace wacce taka ragamar (jagorantar) dayawa cikin Fina fina da take fitowa ciki kuma tabbas za’a iya cewar tabada abinda ake bukata.

‎Yadda Maryam Labarina Ta Yi Fice

‎Shirin da yafara fitowa da ita shine, na ladidi ganin irin rawar da ta taka cikin Shirin dakuma irin gudumawar data bayar ne hakan Yaja hankalin wannan fitaccen daraktan masana’antar kannywood me suna mallam aminu saira har yasata a fim din sa mai suna labarina.

‎duk dacewar maryam labarina ta fito a wasu  fina finai kamin Shirin labarina Amma Shirin labarina tabbas shine wadda ya kawo mata shahara dakuma sanuwa sosai masana’antar kannywood dama wajen masana’antar.

‎shirin labarina ne Shirin dayasa sa ta zama sananniya a fadin arewacin Najeriya, har ma mutane da dama suka daina kiranta da sunanta na asali, suka koma kiranta Maryam Labarina musamman ganin itace taja ragamar fim din.

Maryam labarina
Fatima Hussaini a wajen daukar fim din Dammy & ammy

‎Aikace-Aikacenta

Bayaga kasancewar Fatima Hussaini jarumar fim, takasance mai shirya fim Kuma marubuciya sannan tana fitowa a bidiyon wakokin tareda mawaka wadanda ake daurawa a manhajar YouTube.

‎Fina-Finai da Series : Jerin Fina Finain  Maryam Labarina  Sun Hada da :

Fina finain Maryam labarinaKamfanin Daya shirya
Sirrin kyauMazaje Ne
FatakeUk entertainment
Manyan mataAbdul entertainment
Jamilun jiddaMaishadda global resources
Uwar gidaASA Movies
Sirrin kyauMazaje Ne
LabarinaSaira Movie
Wata ShidaMuryar Hausa Tv
AmaryaSadau Picture Tv
Makarantar farkoArewa Medium

Karanta: CIKAKKEN TARIHIN AISHA SOBA (Shekaru, Aure, Fina-Finai, Wakoki Da Rayuwarta)

Kwarewa Da Basira

‎Fatima Hussaini na daga cikin jaruman da suka hada:

  • Rubutu (script writing)
  • Shirya fim (production)
  • Fitowa a matsayin jaruma

‎‎Iliminta na boko ya taimaka mata sosai wajen kirkirar labarai masu ma’ana da jan hankali.

‎Hadaka Da Jarumai

‎Ta yi aiki tare da manyan jaruman Kannywood a cikin shirye-shiryenta daga cikin su Akwai:

  •  Mazaje ne
  • Usi madobi
  • Sadiq sani sadiq
  • Adam Garba (Raba gardama)
  • Musbahu anfara
  • Baba Sadiq
  • Dan musa Dasauransu.

‎Karin Bayani

Maryam ta fadi cewar asalin yaren iyayenta shine Babur, Kuma Iyayenta Asalin Yan jahar Borno ne dake arewacin kasar Nigeria Amma sauyin wajen aiki yakaisu Jos, Abuja dakuma kaduna.

‎Acewarta tana koyine da sadiya gyale, rahama sadau da Nafisat Abdullahi a mata, cikin maza kuwa Ali nuhu ne abin koyinta.

‎Fatima Hussaini na daga cikin jaruman da ba sa yawan bayyana rayuwarsu ta sirri a kafafen yada labarai.

‎Amma anyi ta rade raden cewar tana soyayya da Jarumin fim din farin wata wato adam garba wadda akafi sani da Raba gardama.

Saide dukka bangagori Biyu sun bayyanawa hakan da abotace kawai a tsakanin su, Wanda Daga bisani Adam garba yayi aure a shekarar 2026.

‎Fatima ta ambaci farida Abdullahi dakuma Aisha soba a matsayin mafiya kusanci da ita a masana’antar kannywood.

Nasarori

Fatima Hussaini ta samu nasarori dadama a masana’antar kannywood cikinsu Akwai:

Tarun kudin shiga dakuma masoya, karramawa ta Pandora award da akai mata a shekarar 2025, sannan tasamu gagarumin mota a Matsayin Kyauta Daga wani masoyin shirye shiryenta.

‎Fatima Hussaini na ba matasa shawara da su:

  • mayar da hankali kan ilimi
  • ‎koyi sana’a kafin shiga fim
  • ‎su kasance masu hakuri da jajircewa

‎Manhaja

‎Kamarde kowani Jarumi dakuma jaruma itama Fatima Hussaini Abbas tanada shafukan sada zumunta dauke da tarun mabiya ga jerin username na Maryam labarina a kowani shafi nata na social media.

‎Instagram: fateeema_hussain

‎Youtube: fateeema hussaini Tv

‎Tiktok: fateeema hussaini

Tarihin Fatima Hussaini

Wannan shine cikakken Bayanai dangane da Tarihin Fatima Hussaini kannypedia tayi dogon nazari wajen kawo muku, ku cigaba da bibiyar mu domin sabunta Bayani lokaci Zuwa lokaci.

Author: Eluthmern

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *