Ga Duk Abinda Ya Kamata Ku Sani Game da Tarihin Bilal Villa
Kannypedia tayi cikakken nazari wajen kawo muku muhimman Bayanai dangane da Tarihin Bilal Villa.
Takaitaccen Bayani
| SUNA | Bilal Villa |
|---|---|
| INKIYA | Bilal Villa |
| SHEKARU | 21 October 1997 ( shekaru 28 Yanxu 2026) |
| AIKI | Waka, barkwanci, kasuwanci |
| JIHA | Kano |
| MAZAUNIN | Kano, Nigeria |
| AURE | Bilal Villa Baiyi Aure Ba ( 2026 ) |
| YARA | Babu |
| WAKOKI | Sama da Ashirin 3 (20+) |
| SOCIAL MEDIA | TikTok: Bilal Villa Facebook: Bilal Villa Instagram: Bilal Villa |

Wanene Bilal Villa ?
Bilal Villa Yakasance Daya Daga cikin shahararrun masu wasan barkwanci na arewacin kasar Nigeria, sannan fitaccen mawakin hausa.
Bilal na Daya Daga cikin matasa masu kananun shekaru wadanda suka samu tarun nasarori a shafukan zumunta musamman tiktok wacce itace sillar haskawarsa.
Bilal de yafara ne da barkwanci Amma Daga baya ya jiya Zuwa wakokin hausa wadda yake rairawa a salo na hausa hip hop.
Bilal Villa asalin Dan jahar Kano ne dake Nigeria Kuma mazaunin garin. A nan aka haifeshi Kuma yayi karatunsa na primary Daga dama secondary a makarantar inter Continental college Amma bai samu kammala sakandarinsa ba sai a makarantar Yan dutse college.
Haihuwa Da Farkon Rayuwa
An haifi Bilal Villa a garin Kano, Kuma cikin garin yayi karatunsa na primari da sakandari dakuma karatun addini. A bangaren karatun boko Bilal ya tsaya ne a Matakin sakandari.
Bayan kammala karatu ne ya Yanke shawarar Fara harkar barkwanci wacce yake da matukar kwarewa akai tin tasowarsa.
Har ila Yau Bilal Villa Yana zaune ne a mahaifarsa ta Kano, sannan mafiya yawancin harkokinsa cikin kanon yake aiwatar dasu.
Manya Daga ciki sune rera Waka, Barkwanci a kafar TikTok, Facebook Instagram, dakuma kasuwanci.
Yadda Ya Fara Aiki
Villa Ya Fara wasan barkwanci (comedy) a shekarar 2021 tin bayan lokacin korona, kasancewar a wansan lokaci mafiya yawancin celebritis Daga Arewa a wannan lokacin suka fito.
Bilal Villa ya fara fitowa ne a kafafen sada zumunta, musamman TikTok, inda yake yin gajerun bidiyoyin barkwanci da nishadantarwa da yaren hausa.
Bayan karbuwarsa a tiktok ne ya fadada izuwa sauran manhajoji dasuka hadada Instagram, Facebook da YouTube inda ya Fara samun tarun dubun nan mabiya tin a wannan lokacin.
Daga bisani suka hade da abokinsa Ngulde Wanda Shima shahararre ne a fannin barkwanci dakuma waka, sai de a wannan lokacin dukkansu Biyun basu Fara waka ba.
Tabbas hadewarsu tasa sun Qara sanuwa matuqa dakuma samun Daukaka sosai duk dacewar a Yanzu sun samu sabani hakan yayi sanadiyar rabuwarsu.
Bilal Villa bai tsaya a iya harkar barkwanci da waka ba, Daga baya ya shiga cikin harkar fim, kasuwanci dakuma streaming.
Film din Bilal Villa na farko itace “The Game” Wanda sukai tareda fareeda Abdullahi shiri da akayishi me gajeren zango Kuma aka daura kan YouTube din jarumar.
Samun Daukaka Bilal Villa
Ya samu shahara sosai ne ta hanyar Bidiyoyin barkwanci da yake wallafawa masu kayatarwa.
Dukda a wannan lokacin Yanada mabiya sosai Amma babu kudi a hannunsa Kuma daukakarsa batai nisa sosai ba.
Bilal Ya samu tarun Daukaka dakuma nasarori ne tin bayan lokaci kadan da Fara wakarsa a shekarar 2021.
Tin bayan fitowarsa wakarsa ta ‘moree’ tareda da shahararren mawakin masarauta da siyasa me suna Naziru wadda akeyiwa laqabi da sarkin waka tin wannan lokacin Duniya tafara yiwa Bilal ganin saqarsa yakai ga cimma.
Haka kuma fitowarsa a fim ‘The Game’ shirin abokiyar aikinsa farida Abdullahi wadda aka haska a shekarar 2025 Kuma ta daura a manhajar YouTube, ya kara nuna hazakar Bilal Villa dakuma kara masa daraja wajen masoya kallan fina finai.
Wakar Bilal Villa
Wakokin Villa nada yawa daga shekarar Daya Fara waka Zuwa Yanzu yayi waka sama da Ashirin 20+ fitattun cikinsu Akwai : Moree, Cele, Hassada, Nema dasauransu.
Jerin Wakokin Bilal Villa Sun Hadada:
| Wakokin Bilal Villa | Sunayen wakokin |
|---|---|
| Abuja jaaa (yeah yeah) | 2026 |
| Hassada | 2026 |
| Moree ft Naziru sarkin waka | 2025 |
| Cigaba | 2025 |
| Sutura ft the_camboi | 2025 |
| Cele | 2025 |
| Takai ft Abba bakaji | 2025 |
| Nema | 2024 |
| Ogah | 2025 |
| Hassada (Acapella) | 2026 |
| Al'ada ft mr442 | 2025 |
| Kudi ft Dan karamin hajiya | 2025 |
| Dangote | 2025 |
| Aboki | 2025 |
| Dance ft key bouy | 2025 |
| Kamarki | 2026 |
| Yar fulani | 2026 |
| Lucky | 2025 |
| Mama | 2025 |
| Love | 2025 |
| Peller | 2025 |
| Tafi tafi ft free boii_shaba | 2022 |

Budurwar Bilali Villa
Ya bayayana karara Bilal Villa Yana soyayya da shahararriya kuma kyakkawar Yar TikTok dinnan mesuna Armani, duk dacewar dafari sun Dan boye alaqarsu Amma Daga baya dukka bangagori Biyu sun bayyanawa duniya hakan.
Dalilin fim din The Game akai ta tinanin ko Bilal Yana soyayya ne da jarumar fim din wato farida Abdullahi Amma Daga bisani duk sun musanta hakan dacewar kawai Shirine dakuma salon Tara mabiya.
Karanta cikakken Tarihin: Cikakken Tarihin Ngulde – (Waka, Aure, Comedy, Award)
Bilal Villa Streaming & Content Creation
Bilal yana daya daga cikin masu live streaming da suka yi suna a Hausa social media, inda yake mu’amala da mabiyansa kai tsaye.
cikin wadanda Bilal yayi stream dasu Akwai: Super wadda akafi sani da uban lissafi, Umar Hamisu ( Yaro mai barkwanci), Alamin dasauransu.
Kasuwanci
Baya ga nishadantarwa, Bilal Villa dan kasuwa ne wanda yake hada sana’o’i daban-daban domin samun kudin shiga.
Bilal Villa a fannin kasuwanci Kuma shine mamallakin Bv fashion wacce ke a jahar Kano.
Dalilin Shahararsa
Bilal Ya shahara ne saboda: Salon barkwanci na musamman Yawan hulda da fans dinsa Kirkire-kirkire a bidiyo Amfani da social media wajen gina suna
Shafukan Sadarwa
Villa made kamar kowani fitaccen Shima yanada shafinsa a yanar gizo mai dauke da miliyoyin mabiya, shafukan zumunta wadanda Bilal yake amfani dasu dakuma username a kowani shafi sune :
TikTok: Bilal Villa
Yanada mabiya sama da Miliyan uku (3 million) a shafin tiktok
Facebook: Bilal Villa
Instagram: Bilal Villa
Villa yanada tarun mabiya samada dubu dari biya a Instagram (500k+)
YouTube: Bilal Villa
Sannan Yana da mabiya sama da dubu saba’in (70k) a manhajar YouTube
Karin Bayani
Bilal Villa na daga cikin matasan dasuka tashi cikin sauri a kafafen sada zumunta, inda ya hada barkwanci, waka, streaming da kasuwanci. Duk da kasancewarsa matashi, ya riga ya kafa suna a duniyar nishadantarwa ta Hausa.
Yana cikin jagorori cikin masu yin waka da salon irin nashi, sannan Kalillan me cikin mawakan hausa suka haura Bilal followers a shafin tiktok.
Tarihin Bilal Villa
Wannan shine cikakken Bayanai dangane da Tarihin Bilal Villa, Kannypedia tayi nazari sosai wajen kawo muku muhimman Bayanai Kuma ingan tattu.
Cigaba da bibiyar mu domin sabunta Bayanao lokaci Zuwa lokaci.
