Cikakken Tarihin Baba Sadiq ( Film, Aure, Rayuwa)

Ga Duk Abinda Ya Kamata Ku Sani Game da Tarihin Baba Sadiq.

Kannypedia tayi cikakken nazari wajen kawo muku muhimman bayanao dangane da Tarihin baba Sadiq.

Takaitaccen Bayani

‎

SUNASadiq Muhammad yelwa
INKIYAbaba Sadiq
SHEKARU21 October 1998 ( shekaru 28 Yanxu 2026)
AIKIJarumin kannywood, content creator
JIHAGombe
KASANigeria
MataBaba Sadiq Baiyi aure ba 2026
YARA Babu
‎FINA-FINAISama da goma 10+
SOCIAL MEDIA USERNAME tiktok: baba sadiq

Instagram: baba Sadiq

Baba sadiq
Jarumi Baba sadiq

wanene Baba sadik Ga Cikakken Tarihin Baba Sadiq

‎Ainahin sunan sa Sadiq Muhammad yelwa Amma  ana kiransa da suna baba sadiq ko Dan gwamnan alfawa sunan da ya samu a Shirinnan mai dogon zango kwana casain.

‎Baba Sadiq matashi ne da ya yi fice a harkar nishadantarwa, musamman a dandalin sada zumunta kamar TikTok, Facebook da Instagram.

Ya shahara sosai wajen kirkirar bidiyoyi masu nishadi, barkwanci da kuma abubuwan da suka shafi rayuwar yau da kullum.

‎anfi sanin Jarumin da sunaye da yake fitowa a fina finai da ake shirya saboda irin rawar da yake takawa cikin Shirin.

Daga cikin sunaye da ake masa take dasu Akwai : baba Sadiq, luqman  Dan gwamnan alfawa sunan daya samo cikin shirin kwana casain, Auwal cikin Shirin labarina, Yusuf gidan cikin Shirin gidan sarauta, safwan a fim din darasi.

‎Haka kuma yana daga cikin sabbin fuska a harkar fim, inda yake kokarin kafa suna a masana’antar Kannywood.

Duk dacewar ba dadewa yayi a masana’antar ba Amma anfi sanin Jarumin ne a fina finai masu dogon zango wadanda ake shirya Kuma a haska a manhajar YouTube.

‎Tin bayan fitowarsa a Shirin labarina tareda jarumai kamar su Sadiq sani sadiq da Kuma fateeema hussaini dasauran.

Inda Baba Sadiq taka rawar Auwal cikin Shirin Daga nan ne jarumin ya Qara samun karbuwa sosai a masana’antar shirya fina finai na kannywood.

Haihuwa Da Asali

‎An haifi Baba Sadeeq a jihar Gombe, dake arewacin Najeriya a can yayi karatunsa na primary dakuma sakandari.

‎Baba Sadiq Yaje jahar Adamawa inda yayi  makarantar a allo (Almajiranci) na tsawon wasu shekaru.

Daga bisani ya koma Jigawa yayi karatunsa na gaba da sakandari a garin kazaure kana ya sake shiga wata makaranta a garin Kano  ya kammala a shekarar 2025 kuma yatafi bautar kasa (nysc)

‎Baba Sadiq Yana da kokari da jajircewa sosai hakan yasa dayawa cikin masu shirya fim suke Nemansa domin yin Aiki tare dashi.

Ainahin yaren Sadiq Muhammad yelwa ( baba Sadiq ) Shine Fulani wadda Jarumin yanaji Kuma Yana iya magana da yaren.

‎Yadda Ya Fara Shahara

‎Acewarsa Bashi da sha’awar harkar a tin yaranta Amma kasancewar yan’uwansa irinsu usman mu’azu, isa ma’azu, yakubu m kumo, saleh yaro, Bilal dasauransu hakan Yaja ra’ayinsa Kuma yabashi damar shiga masana’antar a saukake

‎Baba Sadiq ya shiga harkar fim ne a shekarar dubu Biyu da shatara (2019) da fim kwana casain Shiri mai dogon zango na kamfanin Arewa24 bayan yayi interview a taron audition da aka gudanar a cibiyarsu dake garin kano.

Bayan samun nasarar da baba Sadiq yayi ne, hakan yabashi damar samun shiga Shirin kwana casa’in inda yataka rawar Dan gwamna a cikin Shirin.

Kuma duk dacewar itace Shirinsa na fari Amma yayi matukar kokari sosai yabada abinda ake bukata dari bisani dari hakan yasa daraktoci dadama suka sake Bashi wasu aiyukan.

‎Bayaga harkar fim Baba Sadeeq ya qara samun karbuwa ne ta hanyar TikTok  inda yake saka bidiyoyi masu kayatarwa da jan hankali musamman Wanda ke dauke da Jaruman kannywood mata wadanda suke lokaci.

‎Salon bidiyon jaruman kannywood mata dayake daurawa a fejinsa na tiktok yana daukar hankali Kuma ya sa mutane da dama suka fara bibiyar shafinta nasa tare da yada bidiyoyinsa daga nan ne ya fadada zuwa Facebook inda ya kara samun mabiya da dama.

FINA FINAIN BABA SADIQ

Jerin Fina finain da baba Sadiq ya fito cikinsu kama Daga na masana’antar shirya Fina finan hausa Zuwa Fina finain masu dogon zango wadanda ake daura a manhajar YouTube sun hadada :

Fim din baba SadiqNau'in Fim
Gidan sarautaShirin mai dogon zango ( series fim)
Kwana casa'inShirin mai dogon zango ( series fim)
LabarinaShirin mai dogon zango ( series fim)
DarasiShirin mai dogon zango ( series fim)
Baba sadiq
Tarihin Baba Sadiq

Karanta cikakken Tarihin: CIKAKKEN TARIHIN Khadija Bamalli Banisha Haula (Shekaru, Fina-Finai, Series Da Rayuwarta)

Hadaka

Kasancewar Jarumin ya fito cikin manyan fina finai Kuma dayawa tabbas Babu makawa yayi hadaka tareda wasu Daga cikin manyan Jaruman kannywood kamar su :

  • Sadiq sani sadiq
  • Fatima Hussaini
  • Dan musa
  • Alhassan kwale dasauransu

cikin Shirin labarina saikuma

  • Ali nuhu
  • Umar m sharif
  • dasauransu cikin Shirin gidan sarauta

 

sai cikin Shirin darasi Akwai su

  • Tanimu Akawu
  • isah feroz Khan
  • momi gombe dasauransu.

Rayuwarsa Ta Kullum

‎Baba Sadeeq yana amfani da lokacinsa wajen:

‎Kirkirar sabbin bidiyoyi
Hada kai da sauran creators
‎Mu’amala da mabiyansa
‎Inganta kansa a harkar fim da social media

‎Shawara Ga Matasa

Jarumi baba sadiq ‎Ya kan karfafa gwiwar matasa da cewa: Su yi amfani da baiwar da Allah ya ba su, Su kasance masu hakuri da jajircewa, ‎Su guji amfani da social media ta hanya mara kyau

‎Shafukan Sadarwa

Babu makawa baba Sadiq Yana Daya Daga cikin sabbin Jaruman masana’antar shirya Fina finai na hausa wadanda suke amfanuwa da shafukansu na sada zumunta.

Wadannan sune username na baba Sadiq a shafukansa na yanar gizo:

‎TikTok: Baba Sadeeq

‎Facebook: Baba Sadeeq Official

‎Kammalawa

‎Baba Sadeeq na daga cikin matasan da ke tasowa cikin sauri a fannin nishadantarwa, musamman ta kafafen sada zumunta. Duk da kasancewarsa sabo a harkar fim, yana nuna alamun zai zama babban suna nan gaba idan ya ci gaba da kokari.

Auren Baba Sadiq

Har izuwa shekarar 2026 baba Sadiq Baiyi aure ba, saide anyi ta rade raden cewar suna soyayya da fitacciyar Yar tiktok Kuma Yar kasuwa Nan me suna Rahama Hassan.

Amma Daga bisani dukkan su Biyun sun musanta zargin da ake musu dacewar Babu wani alaqa ta soyayyar a tsakaninsu.

Tarihin Baba Sadiq

Wannan shine cikakken Bayanai dangane da Tarihin Baba Sadiq wadda Kannypedia tayi nazari wajen kawo muku kuci gaba da bibiyarmu domin sabunta Bayani lokaci Zuwa lokaci.

Author: Eluthmern

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *