Wanene Ngulde ? Ga Duk Abinda Ya Kamata Ku Sani dangane Tarihin Ngulde.
A Yau zamu kawo muku cikakken Tarihin Ngulde da duk wasu muhimman bayanai gameda rayuwarsa
Takaitaccen Bayani
| SUNA | Ngulde |
|---|---|
| INKIYA | Sarkin Hoto |
| SHEKARU | 21 October 1998 ( shekaru 28 Yanxu 2026) |
| AIKI | Waka, barkwanci, kasuwanci |
| JIHA | Biu, Jihar Borno |
| MAZAUNIN | Kaduna, Nigeria |
| AURE | Ngulde Baiyi Aure Ba ( 2026 ) |
| YARA | Babu |
| WAKOKI | Sama da Ashirin 3 (20+) |
| SOCIAL MEDIA | TikTok: Ngulde Facebook: Ngulde Instagram: Ngulde |

Cikakken Bayani Akan Tarihin Ngulde
Ngulde fitaccen matashi ne a fagen nishadi Kuma shahararren mawakin hausa, Wanda ya kware a zamanantar da wakokin gargariya na hausa.
Mawaki Ngulde yayi fice a arewacin Nigeria dama sauran nahiyar Africa musamman masoya hulda da kafar zumunta na tiktok.
Ngulde Ya shahara sosai ta hanyar kirkirar bidiyoyin barkwanci da wakoki masu dauke da sako da nishadi, wanda hakan ya sa ya samu karbuwa a zukatan mutane musamman matasa.
Iyayen Ngulde asalin Yan Kauyen Ngulde ne dake garin Biu a jahar borno, Amma an haifeshi a garin maiduguri anan yayi karatunsa na mataki na primary.
Daga bisani iyayensa sukayi kaura izuwa jahar kaduna a kaduna ya kammala karatunsa na matakin sakandari.
Har a Yanzu ibrahim Ngulde yana zaune ne a Kaduna inda yake gudanar da harkokinsa na yau da kullum da kuma kirkirar abubuwan nishadi.
Yadda Ngulde Ya Fara Shahara
Ngulde ya fara samun suna ne ta hanyar wallafa gajerun bidiyoyin barkwanci a shafukan sada zumunta.
Salon barkwancinsa mai sauki da kuma yadda yake amfani da harshen Hausa ya ja hankalin jama’a sosai daga baya, ya hada barkwanci da waka hakan ya kara masa daukaka da shahara a idon masoya da Duniya.
Babu makawa daukakar Ngulde ya ta’allaka ne da shafukan sada zumunta musamman tiktok Wanda shine asalin sillar shaharar sa.
Saide taurarinsa sun kara haskawa ne a wakarsa na Biyu dayayi me suna Tsaf, hakan Yaja hankalina fitaccen mawaki dj Ab har sukai remix na wakar Kuma suka haska wannan video a manhajar YouTube, tiktok, da sarauran wajajen sauraran wakokin zamani.
Yadda Ngulde Ya Yi Fice
Ngulde ya samu gagarumar shahara ne a dandalin: TikTok, Facebook, dakuma Instagram inda bidiyoyinsa suka rika yaduwa (viral), musamman saboda: salon barkwanci na nishadantarwa da yake a nunawa a rayuwar yau da kullum.
Ngulde yana cikin Jaruman hausa tiktok wadanda sukeyin hadaka da fitattun Jaruman hausa harma da Wadanda suke kokarin yin suna.
Haduwar shi da abokinsa Bilal Villa Mawaki Kuma me barkwanci Dan Kano yakan ha karawa dukka bangagori Biyu suna dakuma samun daukaka duk dacewar Daga bisani sun samu matsala sun rabe.
sai de Tin bayan wakar sa dayayi na
- Samarin shaho,
- Dankwali,
- dakuma Riga
Ngulde yasamu nasarar kame Zuciyar duk wani mai Jin wakar hausa musamman masoya irin wannan salo da yake amfani dashi.
Yayinda akai ta ganin mutane Daga kasashen dadama suna hawa wakar suna maimaicinta tare da hawa sound din wakar.
Nasarorin Ngulde A Waka Da Nishadantarwa
Tabbas Ngulde yasamu nasarori dadama a Rayuwarsa, duk da kasancewarsa mai kananun shekaru Amma Ngulde yana gogqyya da manyan mawaka a arewacin kasar Nigeria.
Mawaki Ngulde ya sauya salon wakarsa takoma ta gambara a shekarar 2025 inda yayi wakoki kamar haka Dankwali, Samarin shaho, Riga da Farar kafa.
Duk wadannan wakoki da salon gambara yayisu hakan ya kara masa Daukaka dakuma tarun nasarori da mabiya a shafukan yanar gizo dama dadin duniyar hausa baki Daya.
Daga cikin manyan nasarori da Ngulde tasamu a harkar wakar Akwai kyauttuka da masoya suke masa musamman a wakarsa ta Riga a cikin baiti dayayiwa Yan Daura dake Katsina sanadiyar hakan yasamu kyautar dankareriyar mota ta zamani.
Aikace Aikacensa
Kamar de yadda Mukayi Bayani a baya cewar Ngulde Mutum ne me Hazaka da jajircewa cewa a harkar sa, Daga cikin harkokin da yake (aikace aikacensa) Akwai barkwanci, waka dakuma kasuwanci.
Barkwanci (Comedy)
A fagen barkwanci Ngulde ya yi bidiyoyi da dama da suka shahara a kafafen sada zumunta, inda yake:
kwaikwayon halayen mutane
Nuna matsalolin rayuwa cikin barkwanci
Ilmantar da al’umma ta hanyar nishadi
Wakokin Ngulde
| Wakokin Ngulde | Lokacin da Ngulde Ya saki wakar |
|---|---|
| Riga | 2026 |
| Dankwali | 2025 |
| Samarin shaho | 2025 |
| Tsaf | 2023 |
| Tsaf remix ft Dj Ab | 2023 |
| Sharp sharp ft usman bee & Madox tbb | 2025 |
| Kano 2.0 ft wizkay | 2025 |
| Ruwa ft Ali boss | 2025 |
| Yar gida Daya ft jayboy, Msquare, nnay & feexey | 2024 |
| Munji ft Ado gwanja | 2025 |
| Lala feat maidawa | 2025 |
| Kano ft Mr442 | 2025 |
| Tatata | 2025 |
| Neman magana ft sultan babandala | 2025 |
| Daukaka ft wizkay | 2025 |
| Ummana | 2024 |
| Senetor sani uba ft wizkay | 2025 |
| Sabr | 2025 |
| Haba baba ft jay boy | 2023 |
| Kaduna ft young prblm | 2025 |
| Harara | 2024 |
| Farar kafa | 2026 |

Karanta Cikakken Tarihin :CIKAKKEN TARIHIN BILAL VILLA (Waka, Barkwanci, Aure)
A matsayin mawaki, Ngulde ya fitar da wakoki masu dauke da sako da nishadi, inda yake hada waka da barkwanci domin jawo hankalin masu sauraro.
Cikin wakokinsa da yayi Akwai: Riga, Dankwali, Samarin shaho, Tsaf, Tsaf remix ft Dj Ab, Sharp sharp ft usman bee & Madox tbb, Kano 2.0 ft wizkay, Ruwa ft Ali boss, Yar gida Daya ft jayboy, Msquare, nnay & feexey, Munji ft Ado gwanja, Lala feat maidawa dasauransu.
Hadakar Ngulde Da Sauran Masu Nishadi
Ngulde yana hada kai da wasu masu kirkirar content da mawaka domin kara bunkasa aikinsa da fadada masoyansa.
Hadakar Waka
A hadakar waka, Sarkin Hoto (Ngulde) yayi waka tareda manyan mawaka hausa wadanda suka Shahara sosai musamman a Nigeria da sauran kashen hausa.
Jerin Mawaka Da Ngulde Yayi Waka Dasu
Cikin jerin mawaka da Ngulde yayi hadaka dasu Akwai :
- Dj Ab mawakin hausa rap
- Ado gwanja mawakin hausa musamman fagen Nanaye
- Mr442 mawakin hausa rap
- usman bee mawakin hausa R&p
- feexey mawakin hausa R&B
- sauran mawaka sune Madox tbb
- nnay
- Msquare
- Jayboy
- Prblm
- Wizkay
- maidawa
- babandala dasauransu.
Hadaka Ta Nishadantarwa (Comedy)
kamar de yadda yayi shura wajen yin hadaka a fagen waka, hakama Ngulde yayi fice Wajen hadaka da masu barkwanci da Kuma sauran Jaruman hausa fim wajen yin gajeren video na tiktok da Facebook.
Wasu cikin wadanda yayi hadaka dasu Akwai:
- Bilal Villa
- Dj Ab
- Ado gwanja
- Super uban lissafi
- Adam a zango
- Matiti
- scatter da sauransu
Tasirin Ngulde
Ngulde ya samu karbuwa sosai a kafafen sada zumunta, inda: yake da dumbin mabiya (followers) sama da miliyan 1.
Kuma bidiyoyinsa ke samun dubban miliyoyin views da likes, sannan Ngulde yana daya daga cikin matasan dasuka tashi cikin sauri a fagen nishadi da harkar haka a arewacin Nigeria.
Rayuwarsa Da Salo
Daga cikin halayyar Ngulde shine akwai:
saukin kai; hakan yasa yakeyin hadaka da kananun masu Daukaka domin sasu su shahara. Baiwa da Basira: tabbas kowa yasan Ngulde yanada basira sosai domin yadda yake da kwarewa a dukka fanni Biyu wato nishadi dakuma waka tabbas ba kowa yake da wannan basirar yiba. matashin mawakin Yakan yi amfani da harshen Hausa domin isar da sakonsa ga al’umma cikin sauki.
Shawara Ga Matasa
Ngulde yana karfafa gwiwar matasa da su:
- Yi amfani da baiwarsu.
- Rungumi kirkire-kirkire
- Guji abubuwan da basu dace ba
- mai da hankali wajen neman halal
Shafukan Sadarwa
Kamar kowani Mawaki ko jarumi Shima Mawakin Yana da fejin a shafukan zumunta na zamani Wanda sune ma silar daukakar sa, sannan username nashi a kowani shafi sune kamar haka;
TikTok: Ngulde
Facebook: Ngulde
Instagram: Ngulde
Wadannan kafafen sune sanadiyar sanuwa dakuma samun daukakar Mawaki Ngulde
Kammalawa
Ngulde na daga cikin sabbin hazikan matasa a Arewa da suka kawo sauyi a fagen nishadi ta hanyar amfani da kafafen sada zumunta.
Yana Da jajircewa da kirkira, yana ci gaba da samun daukaka tare da nishadantar da al’umma.
Bisa dogon nazari da Kannypedia tayi Wannan shine cikakken Tarihin Ngulde ku kasance damu domin sabunta Bayani lokaci Zuwa lokaci.
