Cikakken Tarihin G fresh ( Comedy, songs, Aure, Waka) ‎

Ga Duk Abinda Yakamata Kusani Dangane da Tarihin G Fresh

Kannypedia tayi cikakken nazari wajen kawo muku muhimman Bayanai dangane da Tarihin G Fresh Alamin.

Takaitaccen Bayani

SUNAAbubakar Inbrahim
INKIYAGfresh Al'ameen
SHEKARU1987 ( shekararu 39, Yanxu 2026)
AIKIMawaki, Kuma Mai barkwanci
JIHAKano
KASANigeria
MIJISadiya Haruna ( tsohuwar matarsa)
YARA Babu
‎WakokiSama da Talatin 30 +
SOCIAL MEDIAYutube : gfresh Alameen Tv

tiktok: gfresh Alameen

Instagram: gfresh Alameen
Tarihin G fresh alamin
G fresh tareda Ali jita

‎Cikakken Tarihin G Fresh Alamin?

‎G Fresh Alamin  shahararrene a fagen nishadantarwa da Kuma barkwanci, sannan mawakine na hausa musamman a salon Hausa Hip-Hop.

Tabbas Babu makawa Gresh Alamin na cikin manyan Kuma shahararrun daukakakkun hausawa wadanda manhajar TikTok tayiwa gata, domin Babu Wanda yasan gfresh kamin Zuwa TikTok duk dacewar Yana waka a wannan lokacin kamin shigowar tiktok.

G fresh Ya kara samun suna sosai musamman a bangaren yin yawan aure aure da yake Kuma yake nuna zamantakewarsa ya matan nasa, musamman matarsa ta fari mai suna Sadiya Haruna wacce akafi sani da sayyada.

Ta taka muhimmiyar rawa wajen Qara samun daukakarsa a fagen tiktok ganin yadda suka nunawa Duniya irin soyayyar da sukewa junansu sai de Daga bayan sun rabe sakamakon mutuwar aurensu.

Haihuwar G Fresh Da Farkon Rayuwa

Ainahin sunan Gfresh Alameen shine Abubakar Ibrahim, Kuma Yasamu inkyar gfresh ne dalilin waka sunan Alamin kuma sunane na kakansa wadda zamu iya cewar Alamin inkiyace na Gidansu.

Mawaki G fresh Alamin haifaffen Briget ne dake garin Kano a arewacin kasar Nigeria. A Kano yayi karatunsa tin Daga Matakin primari, sakandari haryazuwa Matakin diploma inda yayi karatu a bangaren aikin jarida wato mass com.

Tun Mawaki G fresh yana karami yake nuna sha’awa ga waka da kuma barkwanci, musamman a tsakanin abokai da makaranta Gfresh a tashi ne a mahaifarsa ta Kano Amma Daga bisani harkar waka takaishi Zuwa kasar turai.

Saide Daga baya ya sake dawowa garinsa na Kano wadda haryanzu Yana Nan da harkokinsa.

Yadda G Fresh Ya Fara

‎Mawaki G fresh alamin yayi matukar gwagwarmaya kamin kawo wa Matakin da yake a Yanzu tin a lokacin Babu kafofin sada zumunta na internet.

Ya fara ne da yin waka tin lokacin da ake buka wakoki a kaset din CD a rar-rabawa masu yin dillanci su saya su sayar.

Daga baya G fresh alamin yafara bidiyon barkwanci a TikTok, inda yake kwaikwayon rayuwar yau da Kuma yakeyin abubuwan bandariya.

Gfresh Alameen yafara samun karbuwa sosai a tiktok saboda salon da ya fito dashi na yin barkwanci da Turanci irin na turawa.

Wanda Kuma hakan Yana burge wasu wasu kuma sabanin hakan bisa wannan dalilin mutane da dama suke muhawar a comment section na posting dayayi.

‎Yadda G Fresh Ya Yi Fice

G fresh Alameen ya dade sosai a harkar waka domin yayi wakoki da dama a tarihin rayuwarsa sannan yayi hadaka da mawaka dayawa cikin shahararrun mawakan hausa cikin sun hadada wakarsu da Umar m shareef mai suna Mai Hakuri dakuma wakar Kano to California tareda mawaka irinsu Nomees G, Triple dasauransu.

‎Duk da dadewa G fresh alamin a harkar waka Amma fa bai samu cikakkiyar shaharaba harsai da manhajar TikTok ta bayyana ya Fara abubuwan ban dariya hade da wakokin zamani.

‎Ya fara samun suna ne ta hanyar bidiyoyin TikTok da suka karade dandalin, dakuma wasu kalmomi dayake kirkirowa Kuma mutane suke amfani dasu wajen nasu barkwanci musamman kalmomi Kamarsu :

  • marke
  • sokibututsu
  • hayya hayya
  • zumbur dasauransu.

‎Salon Sa Na Musamman Ya Hada da

  • ‎Haɗa rap da harshen Hausa
  • Barkwanci mai ma’ana
  • Nishadantarwa ga matasa da Yan mata
  • Aikace Aikacen G Fresh

‎Wakokin G Fresh

‎G Fresh Alamin ya fitar da wakoki da dama na CD dakuma online a manhajar YouTube wadanda suka hada da salon Hip-Hop da Afro. Wasu daga ciki sun hada da:

  • Kano to California tareda Nomees G
  • dakuma wakar Zainaba gimbiya tare da Hamisu breaker
  • Halimatu Sadiya tareda Ali Jita
  • Manyan mata
  • rest in peace Lil ameer
  • Kano ce arewa dasauransu.

Jerin Wakokin G Fresh Alamin

‎

Wakokin G fresh alaminLokacin Da Akayi wakar
Maryam ft Ali jita25 March 2025
Darasin Rayuwa ft Dan musa27 March 2025
Yabo13 June 2024
Fati Fati ft Umar m shareef7 July 2023
Maiya Faru ft lilin baba22 March 2023
Ango da amarya29 January 2022
Freestyle feat Ricqy ultra3 January 2023
Kukan kurciya27 December 2022
No pain no Gain5 July 2020
Kano to California ft Nomees G11 October 2021
Fati Fati ft Umar m shareef23 December 2023
Dance Doro ft billy o23 December 2022
Kano ce Arewa16 December 2022
Halimatu Sadiya ft Ali jita2 October 2021
Hapsad22 June 2022
Manyan mata
Can't Back down ft Exboss17 February 2022
Kanawan dabo14 February 2022
White House Family ft Adam A zango $ Zee Preetty17 February 2022
Siyasar kano21 December 2021
Rayuwa ft Umar m shareef29 September 2020
It's Your time ft Annah16 February 2022
Zainaba gimbiya ft Hamisu breaker2 may 2021
Mayan mata20 may 2022
Kasida by sayyada Sadiya Haruna ft g fresh30 May 2023
Zeyara ft Sadiya Haruna3 April 2023
Kano vs Kaduna30 January 2023
Hauwa Amarya20 November 2022
Yahaya bello9 October 2022
Nigeria Muzauna lafiya1 August 2021
Rikicin Duniya27 February 2021
R. I. P. Lil Ameer ft Maryam fantimotee19 February 2021

G fresh
G fresh alamin da tsohuwar matar sa Maryam Nikki

G fresh Alamin tareda Matarsa nikki

Karanta: CIKAKKEN TARIHIN MJ MAI LAYA (Aure, Budurwa, rayuwa) ‎

‎Salonsa Na Nishadi

‎G Fresh Alamin yana amfani da:

‎Hausa + Turanci (mix) Salon turawa, tun ana masa shagube har takai yafara samun dubun Nan mabiya.

Cikin kankanin lokaci G fresh alamin yayi Saurin suna a arewacin Nigeria dama sauran nahiyar Africa baki Daya.

‎G fresh Yayi soyayya Kuma ya auri dayawa Daga cikin shahararrun shafukan tiktok Kamarsu :

  • Sadiya Haruna
  • alpha chales borno
  • Nikki dasauransu

Wannan ya sa yake jan hankalin matasa da Yan mata sosai a social media.

Hadakar Waka

Kasancewar G fresh Daya Daga cikin manyan mawaka na hausa hip-hop wadanda sukayi suna sosai.

Hakan yasa yayai hadaka sosai da wasu mawakan domin kawo waka ta hadin gwiwa.

Jerin Wadanda G fresh Alameen yayi hadaka ta waka dasu Akwai :

  • Umar m shareef
  • Ali jita
  • Hamisu breaker
  • Adam A zango
  • Zee Preetty
  • Maryam fantimotee
  • Nomis gee
  • Sayyada Sadiya Haruna
  • Exboss
  • Annah
  • marigayi Lil ameer
  • Dan musa Gombe
  • Lilin baba dasauran mawakan.

‎Shafukan Sadarwa

Kusan duk Wanda yasan gfresh to Babu makawa yasanshi ne dalilin social media inma Instagram, Facebook, YouTube kokuma musamman tiktok wacce itace tayi silar haskawarsa a duniyar hausawa, wadannan sune jeri username na G fresh Alameen a kowani shafi na yanar gizo.

‎TikTok: (G Fresh Alamin)

‎Instagram: (gfresh_alamin)

‎YouTube: (G Fresh TV)

Shawara Ga Matasa

‎G Fresh Alamin yana karfafa matasa da su:

  • ‎Su yi amfani da basirarsu
  • Su dage wajen aiki
  • Su guji bin hanya mara kyau.

Bisa dogon nazari da Kannypedia tayi Wannan shine cikakken Tarihin G Fresh Alamin ku bibiyemu domin sabunta Bayani lokaci Zuwa lokaci.

Author: Eluthmern

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *