GA duk abinda Yakamata Kusani Game Da Tarihin Dj Ab
Kannypedia tayi Dogon nazari domin kawo muku muhimman Bayanai dangane da Tarihin Dj Ab mawakin Hausa Rap (Gambara).
Takaitaccen Bayani
| AINAHIN SUNA | Haruna Abdullahi |
|---|---|
| INKIYA | Dj Ab |
| SHEKARU | 30 December 1993 ( shekaru 33 Yanzu 2026) |
| AIKI | Waka |
| JIHA | Kaduna |
| MAZAUNIN | Kaduna, Nigeria |
| AURE | Dj Ab Baiyi Aure Ba ( 2026 ) |
| YARA | Babu |
| WAKOKI | Sama da 40 (40+) |
| SOCIAL MEDIA | TikTok: dj_Abba_ Youtube: dj_abba Instagram: dj_Abba_ |

Cikakken Tarihin Dj Ab
haruna abdullahi, wanda aka fi sani da DJ AB ko DJ Abba, fitaccen mawakin Hausa ne na zamani (gambara).
Dayawa na kiransa da sarki a harkar wakar Hausa rap ganin yadda yake hawa kan kida yakuma bada abinda ake bukata.
Dj Ab sannanen Mawaki ne a nahiyar Africa, tin Daga gida arewacin najeria Zuwa kudanci dama kasashen waje masu kin harshen hausa.
Shine Yayan mawakin nan feezey, dakuma G Boy, Tee Swags, Lil Prince kusan dukkan Gidansu mawaka ne.
haihuwa da karatunsa
DJ AB na daga cikin fitattun mawakan Hausa na zamani da suka yi fice a bangaren wakokin gambara.
Ya shahara ne saboda salon wakarsa mai jan hankali da kuma hazakarsa a fagen nishadi.
Ai nahin Sunansa Haruna Abdullahi, Amma Duniya tafi saninsa da suna Dj Ab, sunan Daya samo a sanadin kida da rera waka.
An Haifi Dj Ab a garin Kaduna dake arewacin Nigeria, cikin garin yatashi Kuma yake harkokinsa ya haduwa Yanzu.
Haruna Abdullahi (Dj Ab) yayi karatu tin Daga Matakin primari, sakandari a makarantar makarantar Federal Government College (FGC) Kaduna.
Makwakin yayi karatunsa na digiri a makarantar Ahmadu bello University (Abu) wadda ke a garin Zaria.
India yayi karatunsa na digiri a fannin Quantity Survey yakuma kammala a shekarar 2022.
Ana kallon sa a matsayin daya daga cikin manyan mawakan Arewa na zamani, inda wasu ma ke kiransa da “Sarki” saboda irin tasirin da yake da shi a harkar waka.
Haka kuma, yana daya daga cikin manyan mawakan kungiyar YNS Studio (Yaran North Side).
Yadda Dj Ab Ya Fara Waka
Ya farane da koyan hada kida, ganin yadda yake da ra’ayin wakokin rap na turawa irinsu lil Wayne da Akon.
Daga baya Dj Ab yafara rubuta Wakokinsa na kansa domin rerawa, sannan ya rera a shekarar 2013.
DJ AB ya fara waka tun yana makarantar sakandare (secondary school), inda yake nuna sha’awarsa ga waka tun yana karami.
Sai dai ya fara samun gagarumar daukaka ne a shekarar 2014 bayan fitowar wasu wakokinsa.
Wakokin da suka Daga sunan mawakin Kuma suka sanya ya Shahara guda ukune.
Kuma dukka wakokin ya rerasune karkashin kamfaninsu na Yaran North Side (Yns) wakokin sune:
- Dan Babarsa
- Jallabiya
- Su Baba
Dukka wakokin uku wakoki ne na hadaka tsakaninsa da yan’uwansa Yan cikin kungiyar nasu Kamarsu:
- Tee Swags
- Zayn Africa
- Lil Prince
- Deezell
- Feezy
Kungiyar Yns ta taka muhimmiyar rawa wajen karawa Dj Ab suna da kuma daukaka a harkar waka.
Yadda Dj Ab Ya Yi Fice
DJ AB ya yi fice ne a bangaren wakokin Hausa na zamani (gambara), inda salon wakarsa ya bambanta da na sauran mawaka.
Duk dacewar a lokacin da yafara Waka 2013 Babu fasahar yada wakoki da yanar gizo kamar yadda akeyi a yanzu.
A lokacin tin suna yada wakokinsun ne ta Bluetooth, har yakawo aka Fara daurawa a kananun website ana rabawa mutane link.
Mawaki dj Ab yayi fice sosai ne a sanadiyar cigaba da aka samu Yanzu wajen yada wakoki ta hanyar amfani da shafin Internet.
zuwa Yanzu yanada shafi a account da dama wadanda yake yada Wakokinsa Kamarsu YouTube, audio mack, Instagram da Sauransu.
Kwarewarsa wajen hada wakoki masu dadi da kuma hadaka da manyan mawaka ya sa ya zama daya daga cikin fitattun mawakan Arewa.
Karanta: Cikakken Tarihin Ngulde – (Waka, Aure, Comedy, Award)
Wakokin Dj Ab Karkashin (Yns Studio)
DJ AB ya yi wakoki da dama a karkashin kungiyar YNS Studio (Yaran North Side), wadanda suka taimaka wajen kara masa suna a masana’antar waka.
Daga Cikin Wakokinsa Na Yns Akwai:
- Jallabiya
- Da So Samune
- Ameen
- Waimai Mutum Dan Babansa
- Happy Sallah
- Quarantine
- Siddabaru
- Da sauran wakoki da dama.
Jerin Wakokin Dj Ab
| Jerin Wakokin Dj Ab | Lokacin Sakewa (Date) |
|---|---|
| Shiga (Yabi jiki) | 2026 |
| Dan Tata | 2026 |
| Basuso | 2025 |
| Barcelona | 2025 |
| YNS Cypher chapter 1 | 2025 |
| Khadija | 2024 |
| Lalata Remix ft Gwanja & Cele | 2024 |
| Lalata ft Cele | 2024 |
| Hassada | 2024 |
| Karshe ft khairat Abdullahi | 2024 |
| Sa Ido | 2023 |
| Blow My Mind | 2023 |
| Ki fada ft Zain Africa | 2023 |
| An cuce ni ft Namenj | 2023 |
| Sai ni | 2023 |
| Da Saura | 2023 |
| Keep me safe ft drinking master & boyskido | 2023 |
| Kwapsa ft ice prince & Capture jamil | 2023 |
| Doing my job | 2023 |
| Matsala ft B.O.C Madaki | 2023 |
| Nadama | 2023 |
| The Heist Skit | 2023 |
| Made4u | 2023 |
| Rice Vs Tuwo | 2023 |
| Fish Vs meat | 2023 |
| Noodles Vs Fries | 2023 |
| Haske ft Feezy | 2023 |
| Atiku Okowa | 2023 |
| Shikenan | 2022 |
| Bay Bay | 2021 |
| Masoyiya | 2021 |
| Kudi | 2021 |
| Serious | 2021 |
| Call my phone ft Di'ja | 2021 |
| Ina Da | 2021 |
| Lukuti | 2021 |
| Supa Supa | 2021 |
| Love note ft jigsaw | 2021 |
| Voom | 2021 |
| YNS - Ameen | 2021 |
| Soyayya Dadi | 2020 |
| Crush featuring Deezell | 2020 |
| Da so Samu Ne | 2020 |
| Kin San Ni | 2019 |
| Yi Rawa ft Yung6ix | 2019 |
| Lyrical Bahaushe | 2018 |
| Anzo Wajen | 2018 |
| Babban Yaya | 2018 |
| Daban Ne | 2017 |
| Sugar ft Kennywonder | 2017 |
| Haka | 2017 |
| Totally | 2016 |
| Babarsa | 2016 |

Karanta: CIKAKKEN TARIHIN BILAL VILLA (Waka, Barkwanci, Aure)
Hadakar Dj Ab Da Sauran Mawaka
DJ AB ya yi hadaka da mawaka da dama a masana’antar waka, wanda hakan ya kara masa suna da kuma fadada masoyansa.
Daga cikin mawakan da ya yi aiki tare da su akwai:
- Deezell
- Ali Jita
- Zayn Africa
- Korede bello
- Burna boy
- Morell
- ClassiQ
- B.O.C
- Yung6ix
- Jigsaw
- Tee Swags
- Kheengz
Nasarori Da Karramawa
- DJ AB ya samu nasarori da dama a harkar waka, inda ya sha karɓar kyaututtukan girmamawa a lokuta daban-daban.
- Daga cikin kyaututtukan da ya samu akwai:
- Northern Pandora Awards (2019, 2020, 2022)
- EMPOWER Artists Recognition
- Best Hausa Rapper da wakarsa ta
- Top Northern Rap Collaboration da wakarsa tareda burna boy mai suna
Wadannan nasarori sun nuna irin gudunmawar da yake bayarwa a masana’antar waka ta Arewa
Kafafen Sada Sumunta ( Social Media)
Kamarde duk wani mawakin ko sannanen haka zalika Shima Dj Ab yanada account a shafukan sada zumunta.
Sannan a kowani shafinsa Yana da dubun Nan mabiya wadanda ke San Wakokinsa Daga kasa Nigeria Zuwa sauran kasashen Duniya.
Username na Dj Ab a kowani shafinsa shine :
Tiktok: Dj_Abba_
YouTube: Dj_Abba
Instagram: Dj_Abba_
Kammalawa
A karshe, DJ AB na daga cikin fitattun mawakan Hausa na zamani da suka kawo sauyi a harkar waka.
Ya hada basira da kirkire-kirkire, wanda hakan ya sa ya samu karbuwa a tsakanin matasa da masoya waka.
Tare da nasarorin da ya samu, DJ AB yana ci gaba da zama daya daga cikin manyan taurari a masana’antar waka ta Arewa.
Ku ci gaba da bibiyar Kannypedia domin samun sabbin tarihin jarumai da mawaka a kullum.
