Cikakken Tarihin Amal Umar (Film, Aure, Rayuwa, Waka)

Wacece Amal Umar ? Ga Duk Abinda Ya Kamata Ku Sani Game da Tarihin Amal Umar.

Kannypedia tayi cikakken nazari wajen kawo muku muhimman bayanai dangane da Tarihin Amal Umar.

Takaitaccen Bayani

SUNAAmal Umar
INKIYAAmal
SHEKARU21 October 1998 ( shekaru 28 Yanxu 2026)
AIKIjarumar kannywood, dakuma Nollywood, mai shirya film
JIHAKano
KASANigeria
MIJIAmal Batayi Aure Ba ( 2026 )
YARA Babu
‎FINA-FINAISama da Talatin 30 +
SOCIAL MEDIAYutube : Amal motion picture

tiktok: iamamalumar

Instagram: realamalumar
Amal umar
Hoton Amal Umar

Cikakken Tarihin Amal Umar

Inda Aka Haifi Amal Umar Dakuma Farkon Rayuwar ta

An haifi jaruma Amal Umar a shekarar dubu Daya da dari Tara da casa’in da takwas (1998) a garin katsina dake kasar Nigeria.

Jaruma Amal umar tayi karatunta na Matakin primari har Zuwa makandari duk a jahar katsina nake arewacin Nigeria.

Bayaga karatun boko jarumar tayi zurfin karatun addini matuka sannan jarumar tana cikin shahararrun mata na kannywood da suke da ilimi sosai a dukkan fanni Biyu wato boko da karatun addini.

Yadda Jaruma Amal Umar Ta Shiga Kannywood

Amal tana cikin Jarumai mata na masana’antar shirya Fina finan na kannywood‎ wadanda suke da ra’ayin harkar fim tin a yarantarsu.

Jarumar ta Fara wasan kwaikwayo ne tin a makarantar sakandari inda take fitowa a drama wadanda ake shiryawa a makaranta tareda abokan karatunta.

Ganin irin jajircewar wajen iya drama dakuma Hazaka  fatake dashi hakan yasa jarumar tasamu nasarar shiga masana’antar shirya fina finai na hausa me suna kannywood domin bada nata gudumawar a harkar fim.

‎Jarumi Kuma mawakin nan Yakubu Muhammad shine Wanda yakawo Amal Umar kannywood Kuma yafara sakata a fim cikin Shirinsa tareda abokinsa Mawaki Kuma shahararren Jarumin nan Sani musa Danja.

Jaruma ‎Amal Umar tafiya fitowa a abin tausayi Kuma nitsatsiya wacce ake zalinta kokuma Yar soyayya, mafi akasarin fina finanta na masana’antar kannywood fina finai ne na abin tausayi Kona soyayya.

‎Amal Umar da kanta tace Iyayen gidanta a kannywood sune Yakubu Muhammad dakuma Sani Danja ganin yadda suka tsaya tsayin dake wajen ganin ta samu karbuwa a wajen al’umar hausa.

Izuwa Yanzu Jaruma Amal Umar tana Daya Daga cikin manyan Kuma fitattun Jaruman masana’antar hausa Wanda suke fitowa a manyar fina finai na hausa dama fina finai masu dogon zango ( series ).

Wasu Daga cikin fina finan Amal Umar a masana’antar kannywood Akwai :

  • Hafeez
  • Matan zamani
  • ‎Manyan mata
  • ‎Aisha
  • Mujadala
  • Up North
  • Larai ko jummai
  • ‎Kayi nayi
  • ‎Makota
  • Jabun kudi
  • Sarki goma
  • Zabin raina
  • Abarwa rai dasauransu.

Shigar Amal Umar Nollywood

Babu makawa jaruma amal umar tana cikin Jarumai mata na masana’antar kannywood wadanda ake ganin sunkai makura a harkar fim, domin bawai a iya masana’antar shirya fim na hausa ta tsayaba, ta fadada har izuwa masana’antar fina finai na Nollywood.

Masana’antar Nollywood shine babbar masana’antar fim dake kudanci kasar Nigeria dakuma kasar ghana, wadda ake shirya fina finainsu a yaren turanci.

A wannan karan ma Jaruma Amal Umar ta Fara fitowa a cikin fim din Nollywood ta silar mai gidanta Jarumin nan Yakubu Mohammad.

Kasancewar Shima Jarumin ne Wanda yake fitowa a dukka masana’antu Biyu wato Nollywood dakuma kannywood.

Fina Finain Amal Umar a masana’antar Nollywood sun hadada ; ‎

  • Up north1
  • The herd
  •  voiceless dasauransu.

Nasarori, Daukaka da Amal Umar ta samu a harkar fim

Nasarori

Tabbas izuwa Yanzu Amal tasamu tarun nasarori dakuma Daukaka masu tarun yawa a harkar fim.

Daga cikin nasarori data samu shine samun damar fitowa a dukkan bangagori Biyu dakuma wakoki sannan tana da kamfanin shirya film me suna Amal motion picture.

‎Shahara

Amal Umar tasamu Sahara tin fitowa a manyan fina finai kamar su:

  • naja’atu
  •  Aisha
  • sarki goma zamani goma.

Sannan Fara haduwarta da jarumi Umar m sharif Cikin fim ya kawo mata daukaka sosai a tarihin rayuwarta. ‎

Wakokin Umar m sharif sune suka dagata  hakan yasa tace tafison waka me suna ‘cikin Daya’ Wanda Umar m sharif ya rera.

Fim Din AMAL UMAR Na Nollywood dakuma Kannywood

Kawo Yanzu jarumar ta fito a fina finai na hausa da fim din turanci dadama a cikin kankanin lokaci, fina finan jaruma amal sun haura Talatin 30+, wasu Daga cikinsu sune :

Masana'antaSunan FimNau'in Fim
KannywoodMujadalaFim
kannywoodAishaFim
kannywoodManyan mataFim
kannywoodMatan zamaniFim
kannywoodHafeezFim
kannywoodMakotaFim
kannywoodKayi nayiFim
kannywoodLarai ko jummaiFim
kannywoodJabun kudiFim
kannywoodMakotaFim
kannywoodKayi nayiFim
kannywoodLarai ko jummaiFim
kannywoodAbarwa raiFim
kannywoodZabin rainaFim
kannywoodSarki gomaFim
kannywoodJabun kudiFim
kannywoodMakotaFim
kannywoodwuufShiri mai dogon zango (Series)
kannywoodYar ministaShiri mai dogon zango (Series)
kannywoodSafeeraShiri mai dogon zango (Series)
kannywoodMijinaShiri mai dogon zango (Series)
kannywoodUwar gidaShiri mai dogon zango (Series)
kannywoodMatan gidaShiri mai dogon zango (Series)
kannywoodAbarwa raiShiri mai dogon zango (Series)
kannywoodAna barin halakShiri mai dogon zango (Series)
kannywoodDarasiShiri mai dogon zango (Series)
kannywoodGadan sarautaShiri mai dogon zango (Series)
NollywoodUp northFim
NollywoodThe herdFim
NollywoodShuga naijaFim
NollywoodWing of a doveFim
NollywoodJaru roadFim
NollywoodBlood EnogieFim
NollywoodHussainFim
Amal Umar
Amal tareda Mawaki Dan Musa

Karanta cikakken Tarihin ‎CIKAKKEN TARIHIN FATIMA HUSSAINI (Maryam Labarina) (Shekaru, Aure, Fina-Finai, Rayuwarta)

‎Amal Umar Series fim

Bayaga fitowa a fina finai Amal Umar tana fitowa a Shiri mai dogon zango (series) wasu Daga cikinsu a kamfaninta na Amal motion picture ta shirya wasu Kuma a kamfanin Abubakar Bashir mai shadda, Ali nuhu, Yakubu Mohammad dasauransu.

Cikin fina finai data fito masu dogon zango kamar de yadda Muka irgo Akwai : Mijina tare da Abba xakky Daga kamfanin Amal motion picture,  shirin Safeera tareda yakubu Muhammad series Daga kamfanin Amal motion picture, Yar minista, ‎wuuf Daga kamfanin lilin baba, Ana barin halak Abarwa rai, Matan gida tareda Ali nuhu, sai Kuma Shirin Uwar gida series, ‎Gadan sarauta series tareda Umar m shareef, Shirin Darasi series dasauransu.

‎Hadaka

‎Jarumar ta samu damar fitowa a fina finai tare da mafiya yawancin daga cikin jaruman kannywood kamarsu :

  • ‎Yakubu Muhammed
  • ‎Sani danja
  • ‎Umar M sharif
  • Abdul m sharif
  • Maryam Yahaya
  • Maryam booth
  • Adam A zango
  • Shamsu dan’iya
  • Bilkisu shema
  • ‎Ramadan booth
  • Daddy hikima
  • ‎Rahama sadau ‎Da sauran jarumai.

‎Bidiyon Wakokin Amal

‎Amal Umar tafito a bidiyon waka tare da jarumai dakuma mawaka Kamarsu:

‎Umar m sharif, Hamisu breaker, Ado gwanja, Umar big show, Sadiq sani sadiq, Umar mb, garzali miko, Shamsu dan’iya, Abdul M sharif, musbahu anfara dasauransu.

‎Wasu wakokin Amal umar Wanda ta taka rawa a cikin sune:

‎wakar Wata shida tare da daddy hikima (Abale), wakar Safeera tareda ado gwanja, wakar Mijina series tareda Abba xakky, Majnoon tareda Umar m sharif, Cikin Zuciya tana Kuma tare da garzali Miko, ‎Abarwa rai tareda badaru dadin kowa., Marainiya tareda Abdul m sharif, ‎Inda soyayya tareda Umar big show dakuma Sadiq sani sadiq da sauransu.

‎‎KYAUTAR GIRMAMAWA

‎Jaruma Amal tana cikin Jaruman kannywood dasuka samu kyautar karramawa dayawa cikin karramawarta akwai

‎jaruma mafi jajircewa 2017
‎jaruma me taimakawa jarumai a 2018
‎Fuskar kannywood 2019
‎Fitacciyar jaruma 2021
‎Jaruma mafi nagarta a 2022
Dadai sauransu

‎Saurayin Amal Umar da Sauran Karin Bayanai

‎Ana zargin Amal Umar suna soyayya da Umar m sharif Amma Amal ta musanta hakan, takira alaqarsu a matsayin abota.

‎Acewarta Bata babbar qawa Amma tana da abokai Wanda Aiki yake hadasu, Amma tafi shaquwa da Maryam hayaha.

‎Amal tafi San fitowa da Abdul m sharif a film kamar yadda ta sanar Kuma Abincin datafiso shine danwake.

‎Sannan a duk lokacin da take gida Bata Aiki tafison yin girke girke musamman cake saboda tana sayarwa

‎Amal tabawa masu ra’ayin shigowar shawarar cewa duk abinda ka shigo dace masana’antar kannywood to shi zaka samu alkhairi ko sharri.

‎Kuma ki shiga da Zuciya me kyau karki duba cewar manyan jarumai suna hawa mota Kema kice dole saikin hau. Kede kisa Allah a Ranki.

‎Amal Umar Social Media

‎Youtube : Amal motion picture : 92.7K subscribers a shekarar 2026

‎tiktok: iamamalumar Followers 1.3m, 11m likes a yanzu shekarar 2026

‎Instagram: realamalumar

‎Followers 1.4m shekarar 2026

Tarihin Amal Umar

Bisa dogon nazari da bincike da Kannypedia tayi Wannan shine cikakken Tarihin Amal Umar kasance damu domin sabunta Bayani lokaci Zuwa lokaci.

 

Author: Eluthmern

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *