Ga Duk Abinda Ya Kamata Ku Sani Game da Tarihin Ruky Alim
Kannypedia tayi cikakken nazari sosai wajen kawo muku muhimman Bayanai dangane da Tarihin Ruky Alim.
Takaitaccen Bayani
| SUNA | Rukayya Ahmad Aliyu |
|---|---|
| INKIYA | Ruky Alim |
| SHEKARU | 1996 ( shekaru 30 Yanxu 2026) |
| AIKI | Jarumar Fim, Yar Rawa |
| YARE | Hausa |
| kasa | Cameron da Nigeria |
| AURE | Ruky Alim Batayu Aure Ba ( 2026 ) |
| YARA | Babu |
| fim da wakoki | Sama da Ashirin (40+) |
| SOCIAL MEDIA | TikTok: Rukky_Alim Instagram: Rukky_Alim |

Cikakken Tarihin Ruky Alim
Ruky Alim fitacciyar Jaruma ce a masana’antar shirya fim na hausa wacce akafi sani da kannywood.
Jaruma Ruky tahi Fice sosai a masana’antar kannywood dama wajen masana’antar, domin tanada cikin mata wadanda Allah yayi musu baiwar kyau.
Ruky na Daya Daga cikin Jarumai a masana’antar kannywood wadanda suke da Asali da wasu kasashen.
ita haifaffiyar kasar Kamaru ne (Cameroon) Amma tanada alaqa da kasar Nigeria.
Haihuwarta Da Farkon Rayuwa
Rukky Alim na daga cikin sabbin jaruman Kannywood masu tasowa a masana’antar fina-finai ta Hausa. Ta shahara ne sakamakon fitowarta a bidiyoyin wakoki da kuma wasu shirye-shiryen fina-finai.
An haifi Rukky Alim a shekarar 1996 a garin jaringo dake jahar Adamawa na arewacin kasar Najeriya.
Tayi karatu Daga Matakin primari sakandari duk a jahar taraba, Daga bisani ruki ta koma Zuwa kasar Kamaru a shekarar 2018.
Ruky tashigo Nigeria a shekarar 2020 domin Shiga Masana’antar Kannywood, kai tsaya ya nufi garin Kano domin cika mafarkinta.
Rukky Alim ta fara bayyana a idon jama’a ne a shekarar 2020, lokacin da ta fara fitowa a cikin bidiyoyin wakokin Hausa da ake wallafawa a tashar YouTube channel.
Ruky Alim Tashigo masana’antar kannywood ne ta hanyar wannan Wawaki Kuma Jarumin Nan Garzali Miko.
Yadda Rukky Alim Ta Fara Shahara
Rukky Alim ta fara samun shahara ne a shekarar 2020, lokacin da ta fara fitowa a bidiyoyin wakokin Hausa da ake wallafawa a YouTube.
Fitowarta a wadannan bidiyoyi ya sa mutane suka fara ganinta, musamman saboda kyawunta da kuma yadda take iya taka rawa a cikin video.
Wannan ne ya bude mata hanya shiga harkar fim da kuma kara samun sanuwa a fadin duniya.
bayan suna data samu dalilin fitowarta cikin bidiyon wakoki Ruky ta sake samun damar fitowa a fina finai na kannywood a shekarar 2023.
Yadda Rukky Alim Ta Yi Fice
Rukky Alim ta yi fice ne ta hanyar fitowa a bidiyoyin wakoki da dama tare da fitattun mawaka da jarumai.
Haka kuma, ta samu karin daukaka bayan fitowarta a wani shiri mai dogon zango mai suna “Kaddarata”, Shirin Dadi Hikima.
Wannan shiri ne ya kara daga darajarta tare da janyo mata karin masoya a masana’antar Kannywood.
duk dacewar tafiya fitowa cikin wakokin hausa Amma Ruky nasamu nasarar kame Zuciyar masu shirya Fina fina dayawa.
hakan yasa aka Bata dama domin Bata domin nuna nata bajintar a fagen Fina fina hausa.
daga cikin Fina finai da ruki Alim tafito Akwai Allurar Daga kamfanin 2effect na Sani Danja da Yakubu Mohammed cikin ruwa Wanda itace taja ragama cikin Fim din.
Hakan Yaja ra’ayin babban Mai shirya Fim Mallam Aminu Saira Yabata damar fitowa a Shirin na labarina.
Tabbas Ruky tayi Fice dakuma samun tarun Daukaka a wadannan series Kuma duniyar hausa ta shaida da kwarewar ta.
karanta: Cikakken Tarihin Shamsu Dan’iya (Fina-Finai, Nasarori)
Jerin Fina Finan Ruky Alim
daga cikin Fina finai da jaruma Ruky Alim Ta fito Akwai :
| fim din Ruky Alim | kamadani ko YouTube channel |
|---|---|
| Kaddarata | Abuban Tv |
| India Rai | amart Entertainment ltd |
| Sanda | Daddy Hikima Tv |
| Asin Da Asin | Adam a Zango Official |
| Gwarama | maishadda Global Resources |
| Haram | The Renewed Hope network Trn |
| Rana Dubu | Maidu Global Tv |
| Labarina | Saira Movies, Arewa24 |
| Allurar Cikin Ruwa | Yakubu Mohammed 2effect TV |
| Amaryar Lalle | sadau Pictures Tv |
Wakokin Rukky Alim
Rukky Alim ta fito a bidiyoyin wakoki da dama tun daga shekarar 2020. Daga cikin wakokin da ta fito akwai:
| wakokin Ruky Alim | Date |
|---|---|
| Tauraro Na | 2025 |
| Yahoo boy | 2023 |
| A Raina kayi Shimfida | 2025 |
| Gidan sarauta | 2023 |
| Darasul Auwal | 2023 |
| Yalon Kati | 2023 |
| Mai kishina | 2024 |
| Amira | 2021 |
| Da Yarda | 2021 |
| Soyayya | 2023 |
| wacce Nake so | 2022 |
| Nasamu Wacce Nake So | 2025 |
| So Yafi Zuma Dadi | 2020 |
| Ruhina | 2020 |
| Lokacin Mune | 2020 |
| Matan Gidan | 2026 |
| Na Yarda | 2020 |
| Nabaki | 2023 |
| Alkawari | 2023 |
| Rana dubu | 2022 |
| Asalina | 2021 |
| Yar budurwa | 2021 |
| Zomu sasanta | 2020 |
| Zuciya | 2024 |
| Amrah | 2021 |
| Alkawari | 2023 |
| Ruhin Masoya | 2021 |
| Asalina | 2021 |
| Farin Shigace A Soyayya | 2025 |
| Bazakyi butulci ba | 2021 |
| Bugun Zuciya | 2021 |
| Lokacin Mune | 2021 |
| So Gaskiya Ne | 2022 |
| Bazanyi Butulci Ba | 2021 |

- Ruky Wajen Aikin daukar fim
Hadakar Rukky Alim Da Sauran Jarumai
Rukky Alim ta yi hadaka da jarumai da mawaka da dama a cikin bidiyoyin wakoki da kuma shirye-shiryen fina-finai Daga Ciki Akwai :
Wakar tauraro na tareda Adam a Zango Tashigo kannywood ne ta hanyar jarumi garzali Miko.
Wakar umar mb A Raina kayi Shimfida tareda kb international.
Wakar Yahoo boy tareda Diamond Zara da soja boy.
Mai kishina by Sadiq Saleh, wakar tasamu samada makallata milliyan 10 ( 10 million views) a YouTube.
Gidan sarauta ba auta mb boy tareda Adam a Zango, Amal Umar, Khadija Mailumfashi, Zarah Diamond da Azeema.
Darasul Auwal tareda Sadiq Saleh a shekarar 2023 inda wakar tasamu kusa makallata sama da milliyan bakwai (7million views) a YouTube.
Banda kamarki a Duniya tareda sammani AA.
Tafito cikin Wakar Sadiq Saleh ta Yalon Kati a shekarar 2023.
Wakar Amira a shekarar 2021 tareda Sammani AA.
Tafito Tareda da Garzali Miko, Mailumfashi, Hafeeza , maryam kk, Amaryar Tiktok a waka Mai suna Soyayya a shekarar 2023.
Tafito Tareda Garzali Miko a wakar wacce Nake so a shekarar 2022.
A 2020 tafito da Abdul m Shareef a wakar Ruhina.
Gidan sarauta by Nura m inuwa tareda Garzali Miko.
Rayuwar Aure
Dangane da rayuwar aurenta, Rukky Alim ba ta yi aure ba har zuwa yanzu.
Haka kuma, babu wani sahihin bayani daga gareta dangane da wanda take soyayya da shi, ko wani da ta bayyana a matsayin saurayinta a cikin masana’antar Kannywood.
Nasarori Da Tasiri
Rukky Alim na daga cikin sabbin jaruman Kannywood masu tasowa da suka fara samun karbuwa a cikin kankanin lokaci.
Daga cikin nasarorinta akwai:
- Samun mabiya masu yawa a kafafen sada zumunta
- Fitowa a shahararrun bidiyoyin wakoki
- Samun damar shiga shirin Kaddarata
Haka kuma, tana daga cikin matasan jarumai da ke tasiri a zukatan matasa, musamman a shafukan sada zumunta.
Rayuwarta Da Halayenta
Rukky Alim na da halaye masu kyau da suka taimaka wajen samun karbuwa a idon masoya.
- Daga cikin halayenta akwai:
- Saukin kai
- Kyakkyawan mu’amala
- Hazaka a harkar nishadi
Wadannan halaye ne suka sa take samun karuwar masoya a kullum.
karanta: CIKAKKEN TARIHIN FATIMA HUSSAINI (Maryam Labarin)
Shafukan Sadarwa
Kamar sauran jaruman Kannywood, Rukky Alim tana da shafuka a kafafen sada zumunta inda take hulda da masoyanta.
Daga cikin shafukanta akwai:
Instagram: sama da mabiya 1million (a shekarar 2026)
TikTok: sama da mabiya 1million (a shekarar 2026)
Wadannan shafuka ne suka taimaka wajen yada sunanta da kuma kara mata daukaka.
Kammalawa
A karshe, Rukky Alim na daga cikin sabbin jaruman Kannywood masu tasowa da ke da kyakkyawar makoma a gaba.
Ta fara samun nasara tun daga fitowarta a bidiyoyin wakoki zuwa shiga shirye-shiryen fina-finai, kuma tana ci gaba da samun daukaka a masana’antar.
Ku ci gaba da bibiyar Kannypedia domin samun sabbin tarihin jarumai da mawaka a kullum.
