Ga duk abinda Yakamata Kusani Game Da Tarihin Radiya Jibril Jaruma a masana’antar kannywood
Kannypedia tayi cikakken nazari sosai wajen kawo muku muhimman Bayanai game da Tarihin Radiya Jibril.
Takaitaccen Bayani
| SUNA | Radiya Jibril |
|---|---|
| INKIYA | Mane |
| SHEKARU | 3 January 1993 ( shekaru 33 Yanxu 2026) |
| AIKI | Jarumar fim, Yar kasuwa |
| YARE | Hausa |
| Gari | Lagos da Kaduna, Nigeria |
| AURE | Tayi Aure 2026 |
| YARA | Babu |
| Fina finai | Sama da Goma (10+) |
| SOCIAL MEDIA | TikTok: Mamieralaj Instagram: radeeya_Jibril |

Cikakken Tarihin Radiya Jibril
Radiya Jibril Jaruma ce a masana’antar shirya Fina fina hausa wadda ake kira kannywood.
ta baiyana ne a karshen shekarar 2023 cikin masana’antar kannywood takuma samu tarun masoya da daukaka lokaci Guda.
babu shakka Radiya tana cikin mata a masana’antar kannywood wadanda daganinsu kasan Allah yayi musu kyau matuka.
Radiya na Daya cikin Jaruma Hausa wadda suka samu Shahara da daukaka a lokaci Guda cikin masana’antar fim.
Jaruma Radiya Jibril tasamu sanuwa sosai a Shirin ta na fari mai suna So Sirrin Zuciya wadda aka Daukaka 2023.
Ganin rawar da ta taka cikin Shirin hakan yasa dayawa cikin masu shirya Fim a masana’antar sukayi ra’ayin daukota domin sata a nasu Shirin.
Izuwa Yanzu Radiya ta fito a dayawa cikin Fina Finan hausa Kamarsu Dan jarida, Jikokin Mai gari, So sanadi, Zamani Aure dasauransu.
hakan yasa tasamu Daukaka dakuma tarun masoya musamman Daga kasashen Hausawa maso kallan shirye shiryen kannywood.
Haihuwa da Farkon Rayuwa
An Haifi Jaruma Radiya Jibril a garin Lagos dake kudancin kasar Nigeria a shekarar 1993.
Radiya tayi karatu na Matakin primari a garin Lagos kamin Daga bisani ta dawo garin kaduna dake arewacin tacigaba da karatun ta.
Radiya ta karasa Girman tane a jahar Kaduna wajen kakan ninta hakan yasa tatashi da ra’ayin shiga masana’antar shirya Fina finan hausa.
Shigowarta Masana’antar Kannywood
Jarumar takasance tana da ra’ayin harkar wasan kwai kwayo tin tana Yarinya, domin tayi fitowa cikin drama wadanda ake shiryawa a makaranta lokacin tana karatu.
Bayan kammala karatun ta ne tayiwa Yar uwarta Bayani Akan ra’ayinta na shiga kannywood saboda tasan tanada alaqa da Wasu Daga Cikin masu shirya Fim a kannywood.
Radiya tasamu nasarar shigowa a shekarar 2023 da taimako Yar uwarta, Inda tafara fitowane cikin Shiri mai suna So Sirrin Zuciya.
Irin gudumawa data bayar cikin Shirin ne ya Nuna cewar tabbas Jaruma Radiya Jibril Zara iya.
Sannan lokaci Daya fuskar jarumar Yasanu a masana’antar kannywood dama wajen masana’antar har kasashen dake makwabtaka da Nigeria.
Daukakar Radiya Jibril
Radiya Jibril tasamu sanuwa da daukaka lokaci Guda tin bayan fitowar tareda fitaccen jarumin kannywood Ali Nuhu.
Inda Ya Fito da ita cikin wakar Abdul D one Mai suna CIZA DANI, wakar ta taka muhimmiyar Rawa wajen samun daukakarta.
tin Daga Nan Radiya ta qara samun Daukaka Kuma shafukanta na sada zumunta ( social media account) dukka suka samu tarun followers.
daga Nan Kuma tafara citowa cikin manyan fina Finai na masana’antar cikinsu harda Fina finai masu dogon zango (series film).
haduwar Jaruma Radiya Jibril da jarumi Ty shaba Inda suka gabatar da Shiri Ga kamfanin Indomie wadda suke gabatar da mutane domin hira dasu duk sati.
Hakan ya kara mata Daukaka sosai har ta Fara gogayya da Wasu Jarumai matan kannywood din wajen samun kudaden shiga.

Jerin Fina Finan Radiya Jibril
| Jerin Fina Finan Radiya Jibril | Kamfani ko YouTube channel |
|---|---|
| Aisha Humaira | Abnur entertainment |
| Matan Gida | maishadda Global Resources |
| Balaraba | maishadda Global Resources |
| Dan Jarida | maishadda Global Resources |
| Jikokin Mai gari | M Soja Concept |
| Goje | Kannywood Film |
| Wani dare | Al-Rahuz Films Production Limited |
| So sanadi | Arewa24 |
| Zamani Aure | Bifa Studios |
| so Sirrin Zuciya | Hikima Hausa Tv |
karanta: Cikakken Tarihin Ruky Alim (Fina-Finai, Wakoki, Aure)
Hadaka
Matan Gida tareda Ali Nuhu, Aisha Najamu, Sadiq sani sadiq, Rabiu Rikadawa, Falalu A Dorayi Dasauransu.
Aisha Humaira tareda Jarumi Adam Garba
Wani dare Shiri mai dogon Zango tareda Ibrahim Maishinku, Sadiq sani sadiq
Balaraba hausa series tareda Adam Garba , Shamsu dan’iya, hadizan saima Umar m sharif, Aminu sharif momo dasauransu.
Auren Radiya Jibril
Radiya Jibril Tayi Aure a akaro na Biyu duk dacewar aurenta na fari kamin shigowar ta masana’antar kannywood tayishi.
Amma tayi aura ne a ranar 31 May 2026 duk dacewar tana tsaka da tashe a masana’antar.
Lokaci Daya akaga Jaruma Radiya Jibril tayi sanarwar yin aurenta a shafukan na sada zumunta ( Instagram, tiktok, Facebook).
Ta Kuma nuna farin cikinta tareda Godewa Abokan aikinta na masana’antar shirya Fina finan hausa dakuma yaba irin Zamani takewarsu.
Kamin Yin aurenta anyi ta rade raden cewar tana soyayya ta Jarumi Ty shaba saide Radiya Jibril ta Musa hakan takuma ce a matsayin uban gidanta yake.
Shafukan Zumunta
radiya Jibril tasamu sanuwa sosai lokaci Daya a kafafen zumunta musamman Tiktok da Instagram.
tanada tarun masoya wadanda suke bibiyarta a shafukanta, username na Radiya Jibril sune kamar haka
TikTok: Mamieralaj
Instagram: radeeya_Jibril
karanta: Cikakken Tarihin Khadija Bamalli (Banisha Haula)
Kammalawa
A karshe dai zamu iya cewa Radiya Jibril tana Daya cikin Jaruman masana’antar shirya Fina finai da suka Shahara lokaci Daya.
Sannan Radiya Jibril tana Daya Daga cikin Jaruman kannywood mata wadanda suka Zabi yin Aure a lokacin da suke tsaka da tashensu duk dacewar irinsu kadanne.
Ku ci gaba da bibiyar Kannypedia domin samun sabbin tarihin jarumai da mawaka a kullum.
