Ga Duk Abinda Yakamata Kusani Dangane da Tarihin G Fresh
Kannypedia tayi cikakken nazari wajen kawo muku muhimman Bayanai dangane da Tarihin G Fresh Alamin.
Takaitaccen Bayani
| SUNA | Abubakar Inbrahim |
|---|---|
| INKIYA | Gfresh Al'ameen |
| SHEKARU | 1987 ( shekararu 39, Yanxu 2026) |
| AIKI | Mawaki, Kuma Mai barkwanci |
| JIHA | Kano |
| KASA | Nigeria |
| MIJI | Sadiya Haruna ( tsohuwar matarsa) |
| YARA | Babu |
| Wakoki | Sama da Talatin 30 + |
| SOCIAL MEDIA | Yutube : gfresh Alameen Tv tiktok: gfresh Alameen Instagram: gfresh Alameen |

Cikakken Tarihin G Fresh Alamin?
G Fresh Alamin shahararrene a fagen nishadantarwa da Kuma barkwanci, sannan mawakine na hausa musamman a salon Hausa Hip-Hop.
Tabbas Babu makawa Gresh Alamin na cikin manyan Kuma shahararrun daukakakkun hausawa wadanda manhajar TikTok tayiwa gata, domin Babu Wanda yasan gfresh kamin Zuwa TikTok duk dacewar Yana waka a wannan lokacin kamin shigowar tiktok.
G fresh Ya kara samun suna sosai musamman a bangaren yin yawan aure aure da yake Kuma yake nuna zamantakewarsa ya matan nasa, musamman matarsa ta fari mai suna Sadiya Haruna wacce akafi sani da sayyada.
Ta taka muhimmiyar rawa wajen Qara samun daukakarsa a fagen tiktok ganin yadda suka nunawa Duniya irin soyayyar da sukewa junansu sai de Daga bayan sun rabe sakamakon mutuwar aurensu.
Haihuwar G Fresh Da Farkon Rayuwa
Ainahin sunan Gfresh Alameen shine Abubakar Ibrahim, Kuma Yasamu inkyar gfresh ne dalilin waka sunan Alamin kuma sunane na kakansa wadda zamu iya cewar Alamin inkiyace na Gidansu.
Mawaki G fresh Alamin haifaffen Briget ne dake garin Kano a arewacin kasar Nigeria. A Kano yayi karatunsa tin Daga Matakin primari, sakandari haryazuwa Matakin diploma inda yayi karatu a bangaren aikin jarida wato mass com.
Tun Mawaki G fresh yana karami yake nuna sha’awa ga waka da kuma barkwanci, musamman a tsakanin abokai da makaranta Gfresh a tashi ne a mahaifarsa ta Kano Amma Daga bisani harkar waka takaishi Zuwa kasar turai.
Saide Daga baya ya sake dawowa garinsa na Kano wadda haryanzu Yana Nan da harkokinsa.
Yadda G Fresh Ya Fara
Mawaki G fresh alamin yayi matukar gwagwarmaya kamin kawo wa Matakin da yake a Yanzu tin a lokacin Babu kafofin sada zumunta na internet.
Ya fara ne da yin waka tin lokacin da ake buka wakoki a kaset din CD a rar-rabawa masu yin dillanci su saya su sayar.
Daga baya G fresh alamin yafara bidiyon barkwanci a TikTok, inda yake kwaikwayon rayuwar yau da Kuma yakeyin abubuwan bandariya.
Gfresh Alameen yafara samun karbuwa sosai a tiktok saboda salon da ya fito dashi na yin barkwanci da Turanci irin na turawa.
Wanda Kuma hakan Yana burge wasu wasu kuma sabanin hakan bisa wannan dalilin mutane da dama suke muhawar a comment section na posting dayayi.
Yadda G Fresh Ya Yi Fice
G fresh Alameen ya dade sosai a harkar waka domin yayi wakoki da dama a tarihin rayuwarsa sannan yayi hadaka da mawaka dayawa cikin shahararrun mawakan hausa cikin sun hadada wakarsu da Umar m shareef mai suna Mai Hakuri dakuma wakar Kano to California tareda mawaka irinsu Nomees G, Triple dasauransu.
Duk da dadewa G fresh alamin a harkar waka Amma fa bai samu cikakkiyar shaharaba harsai da manhajar TikTok ta bayyana ya Fara abubuwan ban dariya hade da wakokin zamani.
Ya fara samun suna ne ta hanyar bidiyoyin TikTok da suka karade dandalin, dakuma wasu kalmomi dayake kirkirowa Kuma mutane suke amfani dasu wajen nasu barkwanci musamman kalmomi Kamarsu :
- marke
- sokibututsu
- hayya hayya
- zumbur dasauransu.
Salon Sa Na Musamman Ya Hada da
- Haɗa rap da harshen Hausa
- Barkwanci mai ma’ana
- Nishadantarwa ga matasa da Yan mata
- Aikace Aikacen G Fresh
Wakokin G Fresh
G Fresh Alamin ya fitar da wakoki da dama na CD dakuma online a manhajar YouTube wadanda suka hada da salon Hip-Hop da Afro. Wasu daga ciki sun hada da:
- Kano to California tareda Nomees G
- dakuma wakar Zainaba gimbiya tare da Hamisu breaker
- Halimatu Sadiya tareda Ali Jita
- Manyan mata
- rest in peace Lil ameer
- Kano ce arewa dasauransu.
Jerin Wakokin G Fresh Alamin
| Wakokin G fresh alamin | Lokacin Da Akayi wakar |
|---|---|
| Maryam ft Ali jita | 25 March 2025 |
| Darasin Rayuwa ft Dan musa | 27 March 2025 |
| Yabo | 13 June 2024 |
| Fati Fati ft Umar m shareef | 7 July 2023 |
| Maiya Faru ft lilin baba | 22 March 2023 |
| Ango da amarya | 29 January 2022 |
| Freestyle feat Ricqy ultra | 3 January 2023 |
| Kukan kurciya | 27 December 2022 |
| No pain no Gain | 5 July 2020 |
| Kano to California ft Nomees G | 11 October 2021 |
| Fati Fati ft Umar m shareef | 23 December 2023 |
| Dance Doro ft billy o | 23 December 2022 |
| Kano ce Arewa | 16 December 2022 |
| Halimatu Sadiya ft Ali jita | 2 October 2021 |
| Hapsad | 22 June 2022 |
| Manyan mata | |
| Can't Back down ft Exboss | 17 February 2022 |
| Kanawan dabo | 14 February 2022 |
| White House Family ft Adam A zango $ Zee Preetty | 17 February 2022 |
| Siyasar kano | 21 December 2021 |
| Rayuwa ft Umar m shareef | 29 September 2020 |
| It's Your time ft Annah | 16 February 2022 |
| Zainaba gimbiya ft Hamisu breaker | 2 may 2021 |
| Mayan mata | 20 may 2022 |
| Kasida by sayyada Sadiya Haruna ft g fresh | 30 May 2023 |
| Zeyara ft Sadiya Haruna | 3 April 2023 |
| Kano vs Kaduna | 30 January 2023 |
| Hauwa Amarya | 20 November 2022 |
| Yahaya bello | 9 October 2022 |
| Nigeria Muzauna lafiya | 1 August 2021 |
| Rikicin Duniya | 27 February 2021 |
| R. I. P. Lil Ameer ft Maryam fantimotee | 19 February 2021 |

G fresh Alamin tareda Matarsa nikki
Karanta: CIKAKKEN TARIHIN MJ MAI LAYA (Aure, Budurwa, rayuwa)
Salonsa Na Nishadi
G Fresh Alamin yana amfani da:
Hausa + Turanci (mix) Salon turawa, tun ana masa shagube har takai yafara samun dubun Nan mabiya.
Cikin kankanin lokaci G fresh alamin yayi Saurin suna a arewacin Nigeria dama sauran nahiyar Africa baki Daya.
G fresh Yayi soyayya Kuma ya auri dayawa Daga cikin shahararrun shafukan tiktok Kamarsu :
- Sadiya Haruna
- alpha chales borno
- Nikki dasauransu
Wannan ya sa yake jan hankalin matasa da Yan mata sosai a social media.
Hadakar Waka
Kasancewar G fresh Daya Daga cikin manyan mawaka na hausa hip-hop wadanda sukayi suna sosai.
Hakan yasa yayai hadaka sosai da wasu mawakan domin kawo waka ta hadin gwiwa.
Jerin Wadanda G fresh Alameen yayi hadaka ta waka dasu Akwai :
- Umar m shareef
- Ali jita
- Hamisu breaker
- Adam A zango
- Zee Preetty
- Maryam fantimotee
- Nomis gee
- Sayyada Sadiya Haruna
- Exboss
- Annah
- marigayi Lil ameer
- Dan musa Gombe
- Lilin baba dasauran mawakan.
Shafukan Sadarwa
Kusan duk Wanda yasan gfresh to Babu makawa yasanshi ne dalilin social media inma Instagram, Facebook, YouTube kokuma musamman tiktok wacce itace tayi silar haskawarsa a duniyar hausawa, wadannan sune jeri username na G fresh Alameen a kowani shafi na yanar gizo.
TikTok: (G Fresh Alamin)
Instagram: (gfresh_alamin)
YouTube: (G Fresh TV)
Shawara Ga Matasa
G Fresh Alamin yana karfafa matasa da su:
- Su yi amfani da basirarsu
- Su dage wajen aiki
- Su guji bin hanya mara kyau.
Bisa dogon nazari da Kannypedia tayi Wannan shine cikakken Tarihin G Fresh Alamin ku bibiyemu domin sabunta Bayani lokaci Zuwa lokaci.
