Cikakken Tarihin Nafisa Abdullahi (Shekaru, Fina-Finai, Aure)

Ga Duk Abinda Yakamata Kusani Game Da Tarihin Nafisa Abdullahi

Kannypedia tayi cikakken nazari wajen kawo muku muhimman Bayanai dangane da Tarihin Nafisa Abdullahi.

SUNANafisa Abdullahi
INKIYANafisa sai watarana
SHEKARU3 January 1992 ( shekaru 34 Yanxu 2026)
AIKIJarumar fim, Yar kasuwa, Mai Daukar Hoto
YAREHausa
GariJos, Nigeria
AURENafisa Abdullahi batai Aure Ba ( 2026 )
YARA Babu
Fina finaiSama da Ashirin
(20+)
SOCIAL MEDIATikTok: nafeesat_official
‎Instagram: Nafeesat official
YouTube: Nafiseet Abdullahi
Tarihin Nafisa Abdullahi
Nafeesa

Wacece Nafisa Abdullahi ?

Nafisa Abdullahi fitacciyar jaruma ce a masana’antar Kannywood, wacce ta yi fice a harkar fim, daukar hoto, kasuwanci, da kuma shirya fina-finai.

Tana Daya cikin Manyan Jarumai mata a masana’antar shirya Fina finan hausa wadanda suka dade suna bada gudumawar Kuma Yar Yanzu ake yi dasu.

Nafisa Abdullahi fitacciyar a masana’antar domin dole ne kasako ta a lissafi Idan zaka jero matan kannywood uku wadanda suke da kwarewa a harkar.

Itace Jaruma cikin Fim din labarina season 1 Kuma itace silar karbuwar fim din abin Nan Daga baya Jaruma Fati washa ta karbi wajena.

Nafisa Abdullahi ce jarumar Fina finan hausa da sukafi tashe irinsu Sai watarana, Abdul Malik, Gaduhu Ga Haske, Ahlul Kitab dasauransu.

Cikakken Tarihin Nafisa Abdullahi

An haifi Nafisa Abdullahi a ranar 23 ga watan Janairu, 1992 a garin Jos, jihar Plateau, Najeriya.

Ta fara karatunta a makarantar Air Force Private School da ke Jos, sannan ta ci gaba a Government Girls Secondary School, Dutse da ke Abuja.

Daga bisani, ta halarci jami’a a garin Jos, inda ta kara zurfafa iliminta, Daga nanne nafisa tashigo masana’antar shirya Fina finan hausa.

Daga baya, Nafisa Abdullahi ta kara samun ilimi a fannin daukar hoto (photography) a wata jami’a a London, kasar Ingila, wanda hakan ya kara mata kwarewa a bangaren kirkire-kirkire.

Yadda Nafisa Abdullahi Ta Fara Fim

Nafisa Abdullahi ta fara fitowa a fim tun tana da shekaru 18 a duniya.

Ta fara ne da fim ɗinta na farko mai suna “Sai Wata Rana” a shekarar 2010, wanda kamfanin FKD Production na jarumi Ali Nuhu ya shirya.

A cikin wannan fim, ta fito tare da manyan jarumai kamar:

  • Ali Nuhu
  • Adam A. Zango
  • Fati Washa
  • Lawal Ahmad

Wannan fim ne ya bude mata hanya zuwa daukaka tare da haskaka tauraron ta a masana’antar Kannywood.

Jerin Fim Din Nafisa Abdullahi

Nafisa Abdullahi fimsYouTube channel
KaddaraAbnur entertainment
SultanaCD, DvD
LabarinaSaira movies, Arewa24
Blood and HennaNollywood
Dan Marayan ZakiCD, DvD
Madubin dubawaAli Nuhu
KamanniAli Nuhu
Yaki a soyayyaCD, DvD
Toron GwiwaNazifi Asnanic
SakayyaCD, DvD
Sai wataranaAli Nuhu
Ruwan jakaraCD, DvD
Munafikin mataCD, DvD
Mai farin jiniFaifayin muwaddat Tv
Yar agadezKabir2ube
Addini ko al'adaHausa Film Tv
Ya Daga AllahAl-Rahuz Films Production Limited
AlloZaria Tv
Baban sadiqkKabir2ube
Ahalil kitabAdam a Zango Official
Auren tagwayeAminu Yabo
Dan almajiriHaifa Investment
Ban ganta baZainaba zee-zee
Yar mulkiKabugawa production
AlkawarinaHausa film Tc
Alhakin kwikwiyoCD, DvD
Badi ba raiTnx Arewa
AlhiniAminu Yobo
DareAl-Rahuz Films Production Limited
Fataken dareDorayi films Tv
Laifin dadiAminu Yobo
Gabar cikin gidaPremium times
Jari hujjaCD, DvD
MutallabCD, DvD
Jani mujeUmar m shareef
ShinazAli Nuhu
MuQabalaUzes multi concepts Tv
Mijin mata biyuKabugawa production
Ranar AireAl-Rahuz Films Production Limited
AurenaZinariya Hausa Tv

Karanta : Cikakken Tarihin Umar M Shareef (Album, Wakoki, Fina-Finai)

Duk dacewar a Yan kwanakin baya Nafisa Abdullahi tadan dakata da fitowa a cikin shirin fim saboda tarewa datayi Zuwa kasar england.

Amma Daga bisani jarumar tadawo Nigeria musamman domin fitowa cikin Shirin labarina Shirin da mallam aminu saira ya shirya.

Kuma aka haska a Tashar Arewa24, cikin Shirin Akwai jarumai kamarsu Nuhu Abdullahi, Rabiu Rikadawa, Fati washa dasauransu.

Nafisa Abdullahi ta fito a fina-finai da dama a tsawon lokacin aikinta kamar de yadda muka lissafa.

Daga cikin fitattun fina-finanta akwai Wanda sukafi Shahara Kamarsu:

Sai Wata Rana Wanda shine Shirinta na fari Kuma tafito tareda manyan Jarumai irinsu Adam a Zango, Ali Nuhu, da Lawan Ahmad

Nafisa Abdullahi tafito tareda jarumai  irinsu Ali Nuhu, Rahama Hassan cikin Shirin  Madubin Dubawa.

Toron Giwa Hallau de ta fitone a tareda Jarumi Ali Nuhu dakuma shu’aibu Lawan Wanda aka Fi sani da  Kumurci.

Ummi tareda Adam a Zango dakuma Ummi Rahab lokacin Rahab tana Yar karamarta

Yar Agadez Tareda Jarumai irinsu Adam a Zango dakuma Zainaba indomie

Ahlul Kitab tareda Adam a Zango

Baban Sadiq tareda Adam a Zango dakuma Sadiq sani sadiq

Fitowarta A Nollywood Da Nasarori

Bayan nasararta a Kannywood, Nafisat

Abdullahi ta shiga masana’antar Nollywood, inda ta fito a fim mai suna “Blood and Henna” a shekarar 2012.

Ta yi wannan fim tare da jarumai kamar:

  • Sadiq Sani Sadiq
  • Ali Nuhu

Fim ɗin ya samu karbuwa sosai, inda aka zabi shi a jerin kyaututtuka sama da guda shida.

Hadakar Nafisa Abdullahi

Nafisat Abdullahi ta yi aiki tare da jarumai da dama a masana’antar Kannywood da Nollywood, wanda hakan ya kara mata kwarewa da kuma daukaka.

Daga cikin jaruman da ta yi hadaka da su akwai:

  • Adam A. Zango
  • Ali Nuhu
  • Sadiq Sani Sadiq
  • Nuhu Abdullahi
  • Ahmed Sadiq
  • Ibrahim Maishunku
  • Da sauran fitattun jarumai a masana’antar.

Nasarori Da Karramawa

Nafisa Abdullahi ta samu nasarori da dama a harkar fim, inda ta karbi kyaututtukan girmamawa daga kungiyoyi daban-daban a Najeriya da duniya.

Daga cikin kyaututtukan da ta samu akwai:

  • City People Entertainment Awards
  • Africa Movie Academy Awards (AMAA)
  • MTN Awards
  • Kannywood Awards
  • Afro Hollywood Awards
  • AMMA Awards

Manyan Kyaututtuka

A shekarar 2013, ta lashe kyautar Gwarzuwar Jarumar Shekara daga City People Entertainment Awards saboda fim ɗin “Ya Daga Allah”

A shekarar 2014, ta samu kyautar Gwarzuwar Jarumar Kannywood daga 1st Kannywood Awards saboda fim ɗin “Dan Marayan Zaki”

Haka kuma a shekarar 2014, ta sake lashe kyautar Gwarzuwar Jaruma daga Africa Movie Academy Awards (AMAA)

A shekarar 2016, ta lashe kyautar Gwarzuwar Jaruma daga 2nd Kannywood Awards

Ta kuma samu karramawa daga City People Entertainment Awards a matsayin Gwarzuwar Jaruma 2017.

Duk da cewa a wasu shekarun (kamar 2014 da 2016) an zabe ta amma bata yi nasarar lashe wasu daga cikin kyaututtukan ba, hakan bai hana ta ci gaba da zama daya daga cikin manyan jaruman mata a Kannywood ba.

Best Actress (Jaruma mafi ƙwarewa) a 9th Africa Movie Academy Awards

Daga Cikin nasarori da ta samu shine Nafisat Abdullahi ta zama daya daga cikin manyan jaruman mata a Kannywood, inda ta fito a fina-finai sama da guda 50.

Nafeesa Abdullahi
Nafisa Abdullahi

Karanta: Cikakken Tarihin Amal Umar (Film, Aure, Rayuwa, Waka)

Yadda Nafisa Abdullahi Ta Yi Fice

Nafisa Abdullahi ta yi fice ne saboda kwarewarta a harkar fim da kuma yadda take iya taka rawa iri-iri.

Ta kasance daya daga cikin jaruman mata da suka fi shahara a Kannywood, inda ta samu karbuwa a Najeriya da kuma kasashen waje.

Haka kuma, kasancewarta mai hazaka a bangarori da dama kamar:

  • Shirya fim
  • Daukar hoto (photography)
  • Kasuwanci

ya kara mata daukaka da bambanta ta da sauran jarumai na cikin masana’antar fim din.

Rayuwarta Da Tafiye-tafiye

Nafisat Abdullahi ta ziyarci kasashe da dama a fadin duniya, wanda hakan ya kara mata kwarewa da kuma gogewa.

Daga cikin kasashen da ta ziyarta akwai:

  • England
  • Dubai (UAE)
  • India
  • Amurka (USA)
  • Da sauran kasashen Afrika.

Kammalawa

A karshe, Nafisa Abdullahi na daga cikin fitattun jaruman Kannywood da suka yi fice a Najeriya da sauran kasashen duniya.

Ta samu nasara sosai a harkar fim, tare da kyaututtuka da dama, wanda hakan ya tabbatar da matsayinta a matsayin daya daga cikin manyan jaruman mata a masana’antar.

Ku ci gaba da bibiyar Kannypedia domin samun sabbin tarihin jarumai da mawaka a kullum.

Author: Eluthmern

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *