Cikakken Tarihin Umar M Shareef (Album, Wakoki, Fina-Finai)

GA duk abinda Yakamata Kusani Game da Tarihin Umar m shareef

Kannypedia tayi dogon nazari sosai wajen kawo muku muhimman Bayanai dangane da Tarihin Umar m shareef.

SUNAUmar Muhammad shareef
INKIYAUmar m shareef
SHEKARU21 October 1989 ( shekaru 37 Yanxu 2026)
AIKIMawaki, Jarumin fim, Mai shirya Fina finai
JIHAKaduna
MAZAUNINKaduna, Nigeria
AUREYana da Aure (Maryam Sunan Matarsa)
YARA3
‎WAKOKISama da dari biyu ( 100+)
FimSama da Ashirin ( 20+)
AlbumSama da Goma ( 10+)
SOCIAL MEDIATikTok: umarmshareef1
‎Facebook: umarmshareef
‎Instagram: umarmshareef
Tarihin Umar m shareef
Mawaki Kuma jarumi Umar m shareef

Wanene Umar M Shareef ?

Cikakken sunansa Umar Muhammad shareef Amma anfi saninsa da sunan Umar m shareef a masana’antar kannywood dama wajen masana’antar.

Umar M Shareef fitaccen mawakin Hausa ne kuma jarumi a masana’antar Kannywood, wanda ya shahara sosai a Najeriya da sauran kasashen Afrika.

Umar Yana Daga cikin manyan mawakan hausa wadanda suka samu Shahara dakuma tarun Daukaka.

Shine mawakin fim din madubin dubawa, garin mu danisa, mai farin jini dama sauran wakokin hausa da aka dade ana saurara a arewacin Nigeria.

Mun kawo muku cikakken tarihin Umar M Shareef, shekarunsa, karatunsa, da kuma yadda ya samu daukaka a harkar waka da fim.

Umar M Shareef na daga cikin shahararrun mawakan Hausa da suka yi fice  masana’antar kannywood dama wajen masana’antar musamman a kasashen hausa.

Ya shahara ne saboda muryar sa mai dadi da kuma wakokin soyayya, tausayi da ma’ana da yake rerewa wadda suka ja hankalin masoya.

An haifi Umar M. Shareef a shekarar 1989 a jihar Kaduna, a karamar hukumar Igabi. Ya taso a Kaduna inda ya fara rayuwarsa.

Dangane da karatunsa, Umar M Shareef ya fara karatun Al-Qur’ani tun yana da kananun shekaru kafin daga bisani ya shiga makarantar boko.

Ya ci gaba da karatunsa har ya kai matakin digiri a Jami’ar Kaduna State University (KASU), inda ya kara bunkasa iliminsa tare da ci gaba da harkar waka.

Fara Wakar Umar M Shareef

Umar m shareef ya dade sosai yana Waka, domin tin kamin shigowar kannywood yake rerewa saide a wancan lokacin wakokin gala yake rairawa.

Shigowarsa masana’antar shirya fim na hausa ne ya sauya masa salon wakarsa izuwa wakokin soyayya dakuma na tausayi.

Umar yakasance Yana waka tin lokacin da ake bugawa a faifayin CD, lokacin Babu cigaba kamar Yanzu.

Daukakar Umar M Shareef

Daukakar Umar m shareef ya farane tin Bayan shigowarsa masana’antar kannywood.

Sanya wakokinsa cikin Fina finai hausa da akeyi ne yasa yafara gogayya da sanannun mawaka tin a wancan lokaci.

Baya ga harkar waka, Umar M Shareef ya yi fice a matsayin jarumi a masana’antar Kannywood, inda ya fito a fina-finai da dama.

Daga Cikin Fina-finan Da Ya Fito Akwai:

  • Mansur
  • mariya
  • Gidan sarauta
  • Hafeez
  • Soyayyara
  • Jinin jikinna
  • Nas (na Adam A. Zango)
  • Da sauran fina-finai da dama.

Umar M Shareef ya fi fitowa a fina-finan kamfanin FKD Production, wanda mallakin uban gidansa ne fitaccen jarumin Nan Ali Nuhu ne.

Haka kuma, shi ne mamallakin Shareef Studio, inda ya samar da fina-finai kamar su:

  • Zarah
  • Jinin Jikina
  • Soyayya ta (series) dasauransu

Wadannan ayyuka sun kara masa daukaka a masana’antar Kannywood sosai da sosai domin tasa ansake sanin fuskarsa, sabanin Jin muryar kadai da akeji cikin Waka.

Jerin Fina finan Umar m shareef

Umar m shareef FilmsChannel YouTube
Kaso a sokaUmar m shareef
NadeeyaRahama sadau
MansoorAli Nuhu
FatiSadiq sani sadiq
Soyayyata (series)Umar m shareef
HafeezAl-Rahuz Films Production Limited
Zabin RaiSmart entertainment ltd
Tsakanin muHausa trend
Na dawo Gare kiAlolo Hausa Tv
Karki manta daniAli Nuhu
Ruwan IdoSadau Pictures Tv
Zainaba AbuBig J
MujadalaMaishadda Global Resources
SareenaSmart entertainment ltd
UmmeetaAlolo Hausa Tv
Hauwa KuluMaishadda Global Resources
NasAdam A Zango Official
MafiyaMaishadda Global Resources
Amaryar lalleSadau Pictures Tv
Gidan sarautaMaishadda Global Resources

Karanta: ‎CIKAKKEN TARIHIN FATIMA HUSSAINI (Maryam Labarin)

M shareef

Hadakar Fina-finai

Umar M Shareef ya yi aiki tare da jarumai da dama a cikin fina-finai, wanda hakan ya kara masa kwarewa da kuma shahara.

Daga Cikin Jaruman Da Ya Yi Hadaka Da Su Akwai:

  • Ali Nuhu
  • Maryam Yahaya
  • Shamsu Dan Iya
  • Maryam Booth
  • Amal Umar
  • Maryam Booth
  • Abdul m shareef
  • Da sauran fitattun jarumai a masana’antar Kannywood.

Yadda Umar M Shareef Ya Fara Waka

Umar M Shareef ya fara waka ne tun yana matashi, kuma farkon sha’awarsa ta waka ta samo asali ne daga soyayya.

Mawaki Umar m shareef ya fara waka ne saboda wata yarinya da yake so, amma bai samu damar bayyana mata ba.

Wannan lamari ne ya sa ya fara rera waka domin bayyana abin da ke cikin zuciyarsa.

Daga nan ne ya fara shiga harkar waka a hankali har ya zama daya daga cikin fitattun mawakan Hausa.

Daukakar Umar M Shareef

Umar M Shareef ya dade yana waka, amma tauraron sa ya fara haskawa sosai a shekarar 2007.

Kadan cewar a wannan lokaci, ya fitar da wakoki da dama a bangarori daban-daban kamar:

  • Soyayya
  • Siyasa
  • Wakokin Aure
  • Tausayi
  • Fadakarwa

Daga Cikin Fitattun Wakokinsa Akwai:

  • Jinin Jikina
  • Mariya
  • Hafiz
  • Madubin dubawa
  • Nafada
  • Inna rasaki
  • Rike
  • Wasika
  • Maryama
  • Kina nesa

Da sauran wakoki da dama da suka kara masa suna a fagen waka.

Jerin Wakokin Umar m shareef Daga 2018 Zuwa 2026

Wakar Umar m shareefDate
Soyayyata visualiser2026
Farko da karshe2026
La la laa2025
Matso kusa2025
Ta rikitani2025
Gurin Zama2025
Na Gamsu2025
Yiriri Guda2026
Z & Y curry2026
Khadeeja2025
Na kamu2025
Kyakkyawar fuska2025
So sanadi2025
Ruwan ido2024
Laifina2024
Inada rabbana2024
Hajiya Farida2024
Ni nakine2024
Naji nagani2024
Tawa2024
Inna rasaki2023
Lokaci yayi2023
Ranar aure na2023
Da Gaskiya2023
Na kamu2023
Dan Hausa2023
Ni naki ne2023
Naji nagani2023
Farin jini2023
Daga ke2023
Dangin Amarya2023
Anyi Aure2023
Baya baya2023
Rayuwata2023
Kan Kauna2023
Zuciya2022
Asma'u2022
Na Yarda dake2022
Rayuwata2022
Aisha2022
Kibani Soyayya2022
Na fada2022
Rikee2022
La ilaha illallah2022
Da soyayya2022
In hakuri bai bakaba2022
Na Yarda dake2022
Kibani Soyayya2022
Shikenan2022
Farin jini2022
Wayyo ni2022
Kyakkyawar fuska2022
Aisha2022
Ta kamani2021
Kina nesa2021
Cikin mafarki2021
Lagwada2021
Wazana Bakaina2021
Na ladidi2020
Fati2020
Ga kyauta2020
Cikin daya2020
Zuciya2020
Fatima Zahra2020
Zeenaru2020
Jamila2020
Bani canzawa2019
Saboda ft korede bello2019
Laifi nane2018
Jani muje2018
Sareena2018
Ruwan Zuma2018
Hawayenki2018
So haka yake2018
In da rai2018
Zuciya ta Ansa kira2018
Ranar rayuwa2018
Bazan barki ba2018
Kaso a soka2018
Dace da juna2018
Guguwar so2018
Babban Rana2018
A Daina batuna2018
Da ganina2018
Burin Raina2018
Bazan Barki ba2018
Kalaman Bakina2018
Tsintuwa2018
Kokoa2018
Barauniya2018
Bazan Rayu2018
Nidake2018
Bude cikin Zuciya2018
Kina nesa2018
Bani canzawa2018
Tafiyata2018
Share hawayenki2018
Kikace Nine2018
Har abada2018
Asiya2018
Yarda2018
So Mai Sonka2018
Majnoon2018
Takamani2018
Nazari2018
Kin Bani So2018
So Haka Yake2018
Bako2018
Abin Godiya2018
Dace2018
Cikin Raina2018
Zo mu Zauna2018
Ruwan Zuma2018
Yaki a so2018
Yaya zanyi2018
Taimaka min2018
Nagode ft Sele Bobo2018
Meera2018
Kin Shiga Raina2018
Kin hadu2018
Gamo dake2018
Maryama2018
Ke Na Bida2018
Yaki A Soyayya2018
Tsuntuwa2018
Ana Dara2018
Azeema2018
Hasashe2018
Ruwan Dare2018
Wasika2018
Auren mu Ba Makawa2018
Bako2018

Karanta: CIKAKKEN TARIHIN AISHA SOBA (Fina-Finai, Wakoki)

Albums Na Umar M Shareef

Umar M Shareef ya fitar da albums da dama a tsawon lokacin da yake waka.

Daga cikin albums dinsa akwai wadanda suka fi sanuwa Akwai.

  • Lokaci yayi
  • Masoya
  • Tsintuwa
  • Kalaman Bakina
  • Bako

Wadannan albums sun taimaka wajen kara masa kwarewa da kuma daukaka a masana’antar waka.

Jerin Wakokin Album na Umar m shareef

Umar m shareef AlbumsDate
Bako2018
Farin jini2022
Lokaci Yayi2024
Masoya2023
Ni Da ke2019
Soyayyata2026
Tsintuwa2018
Kuyi hakuri2023
Kalaman Bakina2023
Babbar Yarinya2023
Umar m shareef
M sharif wajen daukar fim

Hadakar Waka

Umar M Shareef ya yi hadaka da mawaka da dama a cikin wakokinsa, wanda hakan ya kara masa suna da kuma fadada masoyansa.

Daga cikin mawakan da ya yi aiki tare da su akwai:

  • Nura M. Inuwa
  • Abdul D one
  • Salim smart
  • Lilin Baba
  • Meleri
  • Aura mg boy

Da sauran mawaka da dama a masana’antar waka ta Hausa.

Nasarori Da Karramawa

Umar M Shareef ya samu nasarori da dama a rayuwarsa ta harkar waka da fim.

Ya sha karɓar kyaututtukan karramawa daga kungiyoyi daban-daban a cikin gida da waje, wanda hakan ke nuna irin gudunmawar da yake bayarwa a masana’antar nishadi.

Daga Cikin Kyaututtukan Da Ya Samu Akwai:

  • Kannywood Films Awards
  • African Actors Awards
  • Da sauran kyaututtuka da dama.

Tasiri Da Mabiya

Umar M Shareef yana daga cikin mawakan Hausa da suka yi tasiri sosai a cikin al’umma.

Muna iya cewar Yana iya Zuwa na Daya ko na Biyu cikin mawakan da sukafi TASIRI cikin mawakan kannywood.

Umar m shareef Yana da mabiya a kasashe daban-daban a fadin duniya, kuma wakokinsa suna isa ga mutane da dama.

A kafafen sada zumunta ma, yana da dimbin masoya, inda yake da sama da mabiya miliyan 1.6 a Instagram, wanda hakan ke nuna irin karbuwar da yake da ita.

Rayuwarsa Da Iyali

Dangane da rayuwarsa ta iyali, Umar M Shareef yana da mata daya mai suna Maryam, tare da ‘ya’ya biyu: Aliyu, Hafsat

Haka kuma, yana daga cikin jarumai da mawaka da suka ziyarci kasashe da dama a fadin duniya, ciki har da:

  • Saudi Arabia
  • Dubai
  • England
  • Niger
  • Ghana
  • Gabon

Wadannan tafiye-tafiye sun kara masa kwarewa da kuma fadada alakar sa a duniya.

KAMMALAWA

A karshe, Umar Muhammad Shareef na daga cikin fitattun mawakan Hausa da suka yi fice a Najeriya da sauran kasashen Afrika.

Ya hada waka da fim, inda ya samu nasara a bangarori biyu, tare da ci gaba da nishadantar da al’umma.

Tare da kwarewarsa da hazakarsa, Umar M. Shareef yana daga cikin manyan taurari a masana’antar Kannywood.

Ku ci gaba da bibiyar Kannypedia domin samun sabbin tarihin jarumai da mawaka a kullum.

Author: Eluthmern

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *