Cikakken Tarihin Khadija Bamalli (Banisha Haula)

Ga Duk Abinda Ya Kamata Ku Sani Game da Tarihin Khadija Bamalli

Kannypedia tayi cikakken nazari wajen kawo muku muhimman Bayanai dangane da Tarihin Khadija Bamalli.

Takaitaccen Bayani

SUNAKhadija Bamalli
INKIYABanisha Haula
SHEKARU2000 ( 26 years)
AIKIJaruma ( actress )
YAREHausa
MAZAUNINKaduna, Nigeria
AUREKhadija Bamalli batai Aure Ba ( 2026 )
YARA Babu
Fina finaiSama da Biyar
(5+)
SOCIAL MEDIA‎Instagram: realkhadybamalli

‎Tiktok:  officialkhadijabamalli

‎Wacece Khadija Bamalli ?

Khadija Bamalli
Jaruma Khadija Bamalli

‎Kadija Bamalli sabuwar jaruma ce a masana’antar Kannywood wacce ta fara jan hankali bayan fitowarta a cikin wani shahararren Shiri  mai suna “Haula“.

Shirin da akayi a shekarar 2026, wadda jarumi Shamsu dan’iya ya rubuta sannan fitaccen  darakta  Kuma jarumi Ali Nuhu Muhammad ya shirya.

Ainahin sunan ta shine Khadija bamalli Amma ana kiranta da suna Banisha sunan da ta samoshi a shirinta na haula wadda aka haska a shekarar 2026.

‎Jaruma Banisha Ta samu karbuwa sosai cikin kankanin lokaci saboda kwarewarta dakuma rawar da ta taka a Shirin Haula.

Duk dacewar shine shirinta na fari wadda ta Fara fitowa Matsayin wacce ta jagoranta a rayuwar ta na kannywood.

Jaruma Khadija Bamalli tasamu karbuwa tin a fagen haska Shirin Haula ganin yadda Yan jarida da Masu YouTube dakuma tiktokers sukaita yin sharhi dangane da ita dakuma Shirin.

Bayaga harkar fim Khadija Bamalli ta fitowa a wasu Daga cikin wakoki wadanda ake daurawa a manhajar YouTube.

Daga cikin wakoki data fito cikin Akwai wakar mawakin nan ahmerdy me suna Abar Min Ke wadda ya sake a shekarar 2026.

Khadija tasake fitowa cikin wakar mawakin nan Auta mg boy me taken suna Haula wadda ya raira a shekarar 2026 dadai sauran wakokin.

Haihuwa Da Farkon Rayuwa

‎An haifi Khadija Bamalli a jihar Kaduna, dake arewacin kasar Najeriya. Ta taso a cikin iyalai masu son ilimi da tarbiyya, inda ta yi karatunta na firamare da sakandare a garin Kaduna.

Khadija Bamalli taci gaba da karatun har izuwa Matakin digiri Kuma tana Daya Daga cikin Jarumai mata a kannywood wadanda sukai Nissan karatu na boko.

Shekarar haihuwar jaruma Khadija bamalli  shine 2002 a yanzu haka jarumar tana da shekaru ashirin da hudu  (24 years).

Yadda Ta Fara Aiki

‎jaruma Khadija Bamalli tana da ra’ayin harkar Shirin hausa tin tana karama saide Bata samu kikakkiyar daman fadawa ba saboda karatu harsai a shekarar 2026.

‎Daga baya ne ta samu damar shiga harkar fim bayan an zabe ta domin fitowa a cikin shirin haula a shekarar 2026.

Cikin Fina finain da jaruma Khadija Bamalli tayisu Akwai Shirin gidan

  • sarauta
  • kaddara
  • Zafin nema
  • saheeba dasauransu.

‎Yadda Khadija Bamalli Tasamu Karbuwa

‎Jaruma Khadija ta samu shahara ne bayan fitowarta a Shirin Haula duk dacewar itace Shirinta na fari.

Tabbas zamu iya cewar tana cikin manyan jarumai wadanda taurarinsu yayi saurin haskawa lokaci Daya a masana’antar kannywood.

Khadija ta Shahara ne tun kamin fitowar Shirin saboda yadda akayita sharhi akan kyawunta dakuma akan Shirin.

‎A cikin wannan fim, rawar da ta taka ya ja hankalin masu kallo sosai, wanda ya sa aka fara ganinta a matsayin sabuwar tauraruwa mai tasowa a Kannywood.

‎Tiktok da Facebook

‎Tabbas ba makawa jaruma Banisha tayi ficene a sanadiyar Fara yada tallar shirin Haula da akayi tayi a shafukan zumunta.

‎Mamakin yadda aka gabatar da sabuwar fuska Kuma kyakkawar jaruma a babban Shiri Kuma na Jarumi Ali nuhu yasa mutane sukayi yadawa dakuma nasu tsakanin.

‎Jerin Fina Finain Khadija Bamalli

‎

Khadija Bamalli fimNau'in FimKamfani ko channel
HaulaSingle fimAn Ali Nuhu movie
Gidan sarautaShirin mai dogon zango (series)Maishadda global resources
SaheebaShirin mai dogon zango (series)Maishadda global resources
KaddaraShiri mai dogon zango (series)Abnur entertainment
Zafin nemaShirin mai dogon zango (series)Sadiq sani sadiq
A bar min ke ft ahmerdyWakar hausaAhmerdy
Haula ft aura mg boyWakar hausaAuta mg boy

Banisha Haula
Jaruma banisha

Karanta: Cikakken Tarihin Baba Sadiq ( Film, Aure, Rayuwa)

Hadaka Da Jarumai

Zuwa Yanzu jaruma Khadija bamalli (Banisha) tayi hadaka tareda manyan jarumai na masana’antar shirya Fina finan na hausa (kannywood).

Daga cikin Jarumai da tayi aiki dasu Akwai fitaccen Jarumin Nan

  • Adam A zango
  • Adam garba ( Raba gardama )
  • dakuma sadiq sani sadiq dasauransu a cikin shirin Saheeba.

Tayi hadaka da jarumai kamarsu:

  • Umar m shareef
  • Yakubu Muhammad
  • garzali Miko
  • Ramadan booth dasauransu cikin Shirin Gidan sarauta.

Bamalli ta fito cikin Shirin Zafin nema hakan Yabata daman yin hadaka tareda jarumai kamarsu

  • Yamu baba
  • Sadiq sani sadiq
  • tahir I tahir dasauransu.

Sannan cikin Shirin kaddara tayi hadaka da Nafisan Abdullahi, Ibrahim maishinku, zaharadeen sani, falalu a dorayi dasauransu.

‎Kyaututtuka Da Nasarori

‎Saboda sabuwar shiga ce, har yanzu ba ta samu manyan kyaututtuka ba, amma ana kallonta a matsayin jaruma mai haske a gaba.

‎daga cikin nasarori da ta samu shine saurin samun daukaka domin tabbas ba kowace jaruma take samun Shahara a shirinta na fari ba.

Bayaga saurin Shahara Khadija Bamalli tayi sa’ar Fara fitowa tareda jarumi Ali nuhu wadda ake yiwa laqabi da king of kannywood musamman ganin shine Shirinta na fari.

‎Karin Bayani

‎Banisha tana daga cikin jarumai masu son natsuwa da kaucewa hayaniya.

‎Ta bayyana cewa tana son:

‎yin karatu
‎kallon fina-finai
‎da kuma koyon sabbin abubuwa a harkar Fim

Burinta A Kannywood

‎Banisha na da burin zama daya daga cikin manyan jaruman Kannywood a nan gaba, tare da yin aiki da fitattun daraktoci da kuma wakiltar masana’antar a duniya.

‎Shawara Ga Matasa

‎Ta shawarci matasa da su: ‎su dage wajen neman ilimi, su bi mafarkinsu, su kasance masu hakuri da jajircewa

‎Kammalawa

‎Banisha na daga cikin sabbin jarumai masu tasowa a Kannywood a shekarar 2026. Duk da cewa ta fara ne da series guda daya, ta nuna kwarewa da basira da ke nuna cewa tana da kyakkyawar makoma a masana’antar fim ta Hausa.

‎Social Media

Jaruma Khadija Bamalli ta bude account a Instagram dakuma tiktok domin Neman ainahin username nata a dukkan shafukan gasunan kamar haka:

‎Instagram: realkhadybamalli ‎

Tiktok:  officialkhadijabamalli

Saurayin Khadija Bamalli

Ganin yadda jarumar take da kyau da Kuma iya muamalantar abokan aikinta maza, hakan yasa mutane suke ganin cewar Akwai alaqa ta soyayya tsakanin su.

Daga cikin wadanda akai zargin soyayya Mai karfi tsakaninsu Akwai; ahmerdy a lokacin daukar bidiyon wakar abarminke.

Haka zalika an yi rade raden alaqar soyayya tsakanin ta da Shamsu Dan iya lokacin daukar Fim din Haula.

Saide jaruma Khadija Banisha ta karyata dukkanin Jita Jita da ake tayi.

Tarihin Khadija Bamalli

Kasance damu domin sabunta Bayani dangane da Tarihin Khadija Bamalli lokaci Zuwa lokaci.

Author: Eluthmern

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *