Ga Duk Abinda Yakamata Kusani Game Da Tarihin Shamsu Dan’iya.
Kannypedia tayi cikakken nazari sosai wajen kawo muku muhimman Bayanai dangane da Tarihin Shamsu Dan’iya, Karatunsa, Fina finai da Rayuwarsa.
Takaitaccen Bayani
| SUNA | Muhammad Iliya |
|---|---|
| INKIYA | Shamsu Dan'iya |
| SHEKARU | 1990 ( shekaru 36 Yanxu 2026) |
| AIKI | Jarumim fim, Mai Daukar Sauti, Mai shirya Fim |
| YARE | Hausa |
| Gari | Kaduna, Nigeria |
| AURE | Shamsu Dan'iya Baiyi Aure Ba ( 2026 ) |
| YARA | Babu |
| Fina finai | Sama da Ashirin (40+) |
| SOCIAL MEDIA | TikTok: Shamsu-daniya Instagram: Shamsu_daniya |

Cikakken Tarihin Shamsu Dan’iya
Shamsu Dan’iya fitaccen jarumi ne a masana’antar Kannywood wanda ya shahara wajen fitowa a fina-finai da kuma bidiyoyin wakokin Hausa.
Cikakken Sunansa Muhammad iliya Amma anfi saninsa da suna Shamsu Dan iya, sannan ya dade cikin masana’antar ta kannywood.
Suna Shamsu dan’iya sunane na Zuri’a (Family name) hakan yasa yake amfani da ita a cikin masana’antar Kuma da sunan Duniya tasansa.
Shamsu yafara da daukar sauti cikin masana’antar kannywood saboda jajircewa dayayi Yanzu Yana cikin Jaruman masana’antar.
Dan’iya yana cikin dayawa Daga Fina finan masana’antar kannywood wadanda suka Shahara musamman Fina finan kamfanin FKD.
Cikin manyan fina finansa da suka Shahara Akwai Gamu nan de, haula, Sareena, Jaruma dasauransu.
Cikakken Tarihin Shamsu Dan’iya
Shamsu Dan’iya na daga cikin jaruman Kannywood da suka yi fice a harkar fim da kuma bidiyoyin wakoki. Ya shahara ne sakamakon hazakarsa da kuma yadda yake taka rawar gani a fina-finai.
An haifi Shamsu Dan’iya a shekarar 1990 a garin Kaduna dake arewacin kasar Nigeria, inda ya taso kuma ya fara rayuwarsa.
Ana kiran sa da sunan “Dan’iya” ne saboda asalinsa Dan sarauta ne, inda wannan suna ya samo asali daga kakansa wanda yake da lakabin sarauta mai suna Dan’iya.
Dangane da karatunsa, Shamsu Dan’iya ya yi karatun firamare da sakandare a jihar Kaduna.
Daga bisani, ya ci gaba da karatunsa a Maryam Abacha American University Niger (MAAUN), inda ya karanci ilimin aikin jarida (Mass Communication).
Yadda Shamsu Dan’iya Ya Fara Fim
Shamsu ya farane a matsayin mai daukar sauti a masana’antar fim na kannywood kamin Daga baya ya juye Zuwa jarumi.
Uban gidansa a harkar sauti shine Usman ma’azu, shine wadda ya koya masa aikin nadar sound tin kamin yazama jarumi a masana’antar.
A matsayin me daukar sautin Fina finai Shamsu Yayi Aiki tareda daraktoci irinsu Mallam Aminu Saira, Abubakar A.S Maikwai, Ali Nuhu dasauransu.
Shamsu ya kasance cikin manyan masu daukar sound a wancan lokacin Kuma yayi Aiki a manyan fina finai na kannywood.
Cikin Fina finai dayayi aikinsu Akwai Jidda na Aminu Saira, Garinmu da Zafi dasauransu.
Shamsu dan’iya Ya Fara fitowa cikin Fim a masana’antar kannywood ta dalilin Shaharariyar Jaruma Kuma Mai shirya Fim din nan Mai suna Rashida Adamu Abdullahi.
Shamsu Dan’iya ya fara fitowa a fina-finai tun daga shekarar 2006 zuwa 2008, inda aka fara haskaka shi a wani fim mai suna “Sa’a”.
Tun daga wannan lokaci, ya ci gaba da fitowa a fina-finai daban-daban, wanda hakan ya taimaka wajen kara masa kwarewa da kuma shahara a masana’antar Kannywood.
Jerin Fina-finan Shamsu Dan’iya
Shamsu ya dade Yana bada gudumawa a masana’antar shirya Fina finan hausa, sannan yafito cikin dayawa cikin Fina finai.
Wasu Fina finansa anyi sune karkashin kamfanin FKD Mallakin uban gidansa Ali Nuhu, wasu Kuma karkashin kamfanin Abubakar Bashir maishadda, Amart Entertainment ltd dama Sauransu
Daga cikin fitattun fina-finansa akwai:
| Shamsu dan'iya Fim | Kamfani ko YouTube channel |
|---|---|
| Darasi | Jakada Hausa Tv |
| Tazara | double investment |
| Abadan | RR Production Tv |
| Sharhi | Ali Nuhu Movies |
| Haula | Ali Nuhu |
| littafi | Arewa24 |
| karamci | Alolo Hausa Tv |
| Balaraba | Maishadda Global Resources |
| Ummeeta | Alolo Hausa Tv |
| Dan Talaka | Alolo Hausa Tv |
| Barauniyar Amarya | Ali Jita Multi Media |
| Halimatu | Aryan Movies |
| So sanadi | Arewa24 |
| Gangarso | momee Gombe |
| miji na | Amal Motion picture |
| Tagwaye | Nil |
| Alaqa | Ali Nuhu |
| muradi | Uban Harkalla |
| Burin Masoyi | Alolo Hausa Tv |
| kwana bakwai | Smart Entertainment ltd |
| Albishir | Lilin Baba |
| Babbar Tawaga | Alolo Hausa Tv |
| Gamu nan Dai | Ali Nuhu |
| Aisha | mdEnt Tv |
| Daga Dinner | Amart Entertainment ltd |
| Avenger (Hausa Movie) | Arewa Hausa Tv |
| Makota | Amart Entertainment ltd |
| Barista Kabeer | Al-Rahuz Films Production Limited |
| Karki Manta dani | Ali Nuhu |
| Hadin Allah | Ali Nuhu |
| Sareena | amart Entertainment ltd |
| Matar Salim | Hausa Tv |
Yadda Shamsu Da

karanta: Cikakken Tarihin Khadija Bamalli (Banisha Haula)
n’iya Ya Yi Fice
Shamsu Dan’iya ya yi fice ne ta hanyar fitowa a fina-finai da dama da kuma bidiyoyin wakokin Hausa, wanda hakan ya sa ya samu karbuwa da tarun masoya.
Hazakarsa wajen taka rawa da kuma yadda yake bada gudumawa, ya sa ya zama daya daga cikin jaruman da ake yi dasu a masana’antar Kannywood.
Haka kuma, hadakar da yake yi da manyan jarumai ya kara masa daukaka da kuma karuwar masoya a fadin Najeriya da ma kasashen waje.
Hadakar Shamsu Dan’iya
Shamsu Dan’iya ya yi hadaka da jarumai da dama a masana’antar Kannywood, wanda hakan ya kara masa kwarewa da kuma shahara.
Daga cikin jaruman da ya yi aiki tare da su cikin finai a masana’antar kannywood Akwai:
Ali Nuhu, Garzali Miko, Ramadan booth, da Abdul m sharif Cikin fim din Gamu nan dai.
Shamsu dan’iya Tafito a cikin shirin fim tareda Umar M. Shareef, maryam yahaya da Sauransu cikin Fim din Sareena.
Sharhi tareda momee gombe, Ali Nuhu, Abdul m Shareef, real cousin, zaynab Abubakar.
Abadan tareda diamond Zara, Adam garba, Shatu tareda Aisha soba.
Haula tareda Baba Sadiq, Ali Nuhu, da Khadija Bamalli (Banisha Haula).
Darasi tareda Ali Nuhu, Yamu Baba, lawan Ahmad, momee gombe, daddy hikima, amal umar dasauransu.
Dan talaka tareda tynking maigashi dakuma Rayya.
Ummeeta tareda umar m Shareef, Amal umar da Rayya kwana casain.
Balaraba tareda Adam garba, Yusuf Lazio da radeeya jibril.
Karamchi Tareda Rayya kwana casain da Amina indomie.
Barauniyar Amarya tareda Ali jita, Rabiu Rikadawa , farida Abdullahi,
Da sauran fitattun jarumai a masana’antar.
Nasarori Da Karramawa
Shamsu Dan’iya ya samu kyaututtukan girmamawa da nasarori dama a harkar fim.
Daga cikin kyaututtukan da ya karba akwai:
- Fresh Hausa Fulani Awards
- Kannywood Awards
- African Voice Awards
- City People Entertainment Awards
- Da sauran kyaututtuka da dama.
Wadannan nasarori sun nuna irin gudunmawar da yake bayarwa a masana’antar Kannywood.
Rayuwarsa Da Halayensa
Shamsu Dan’iya na daga cikin jaruman da ke da kyakkyawar mu’amala da masoyansa da kuma abokan aikinsa.
Yana da halaye kamar:
- Saukin kai
- Girmama mutane
- Kwarewa a harkar fim
Karanta: Cikakken Tarihin Umar M Shareef (Album, Wakoki, Fina-Finai)
Auren Shamsu Dan’iya an’iya
Shamsu Yayi soyayya da Abokiyar Aikinsa Jaruma Maryama Yahaya saide Daga baya baya sun rabu.
An yi ta rade raden cewar Yana San Yar Mai gidansa Sarki Ali Nuhu, Amma Dan’iya Ya musanta hakan.
daya daga cikin tambayoyin da ake yawan yi masa shi ne “yaushe zai yi aure?”, amma har yanzu bai bayyana wa masoyansa cikakken bayani game da wannan ba.
Dangane da rayuwar aurensa, har yanzu bai fito fili ya bayyana cikakken bayani game da matar da zai aura ba, duk da cewa ana yawan tambayarsa a kan wannan batu.
Kammalawa
A karshe, Shamsu Dan’iya na daga cikin fitattun jaruman Kannywood da suka yi fice a harkar fim Musamman Bangaren Jarumi Ali Nuhu.
Ya fara tun da dadewa, kuma ya samu nasara ta hanyar jajircewa da kuma hazaka, wanda hakan ya sa ya zama daya daga cikin jaruman da ake girmamawa a masana’antar.
Ku ci gaba da bibiyar Kannypedia domin samun sabbin tarihin jarumai da mawaka a Koda yaushe.
